Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna da takwarorinsa na Algeria ta Tanzania

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya tattauna da ministan harkokin wajen ƙasar Algeria Ramtane Lamamra, da ministar harkokin wajen Tanzania Liberata Mulamula.

Yayin tattaunawa da Lamamra, wanda ke ziyarar aiki a ƙasar Sin, Wang ya bayyana cewa, baya ga ƙasashen dake nuna damuwar game da abubuwan dake wakana a shiyyoyin duniya, akwai kuma ƙasashe da dama kamar Sin da Algeria da suke da daɗaɗɗen tarihi na girmama zaman lafiya da adalci.

Ya yi kira ga irin waɗannan ƙasashen da su hada hannu, kana su ƙarfafa haɗin kai domin daga matsayin ayyukan inganta tafarkin demokaradiyya a bisa tsarin hulɗar ƙasa da ƙasa.

Lamamra ya ce, ƙasar Algeria ta yabawa matsayar da ƙasar Sin ta ɗauka game da rikicin Ukraine, kuma ta yi amanna cewa salon da ƙasar Sin ke bi, wanda ya shafi goyon bayan tabbatar da adalci a matakin ƙasa da ƙasa, da kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da tsaro, su ne hanyoyi mafi dacewa kuma masu cike da ƙwarin gwiwa.

A yayin tattaunawa da Mulamula ta kafar bidyo, Wang ya bayyana cewa, abokantakar ƙasashen Sin da Tanzania ta yi tasiri a zukatan al’umma. Ya ce ƙasar Sin tana burin zurfafa huldarta da Tanzania zuwa matsayin hulda mafi muhimmanci kuma mai kyakkyawar makoma.

Mulamula, wacce ke ziyarar aiki a ƙasar Sin ta kafar bidiyo, ta bayyana cewa, ƙasar Tanzania a shirye take ta gina hulɗarta da ƙasar Sin zuwa wani sabon matsayi ƙarƙashin ruhin haɗin gwiwar Sin da Afrika.

Fassarawa: Ahmad Fagam