Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna ta wayar tarho da babban jami’in EU

CRI HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, jiya Litinin ya tattauna ta wayar tarho da Josep Borrell, babban wakilin ƙungiyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin ƙasashen waje da manufofin tsaro.

A yayin tattaunawar tasu, Borrell ya bayyana ra’ayi da matsayin ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), kan halin da ake ciki a ƙasar Ukraine, inda ya ce, abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne tsagaita buɗe wuta tare da kauce wa hasarar rayuka. Yana mai cewa, EU na goyon bayan warware matsalar ta hanyar yin shawarwari.

A nasa ɓangare kuwa, Wang Yi ya ce, ƙasar Sin ta koka kan yadda halin da ake ciki a ƙasar Ukraine ya kai ga wannan mataki, yana mai cewa, takunkumai ba za su warware matsalolin ba, kuma ƙarin sanya takunkuman babu abin da za su haifar illa ƙara dagula lamarin.

Wang ya ce, abu mai muhimmanci a yanzu, shi ne kauce wa matsalar jin kai. Ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta fito ƙarara inda ta gabatar da wani shiri mai ƙunshe da matakai shida na daƙile matsalar jin kai a ƙasar Ukraine, da nufin inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen duniya, don kauce wa taɓarɓarewar yanayin jin kai a Ukraine.

Ya ce, yana fatan ƙasashen duniya, za su goyi bayan ƙasashen Rasha da Ukraine, don yin shawarwari na gaskiya, wanda ba kawai za a ci gaba da yi a nan gaba ba, har ma za a kai ga tsagaita buɗe wuta, da kawo ƙarshen rikice-rikice, har a kai ga tabbatar da zaman lafiya.

Fassarawa: Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *