Xi Jinping ya zanta da shugabannin Faransa da Jamus

Daga CRI HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta kafar bidiyo da shugaba Emmanuel Macron na faransa, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da yammacin Talatar nan, inda suka maida hankali ga tattauna yanayin da ake ciki a ƙasar Ukraine.

Yayin zantawar ta su, shugaba Macron da Mr. Scholz, sun gode wa gudummawar ƙasar Sin, don gane da tallafa wa manufar samar da agajin jin kai, sun kuma bayyana aniyar su ta ƙarfafa sadarwa, da tsare tsare tare da ɓangaren Sin, domin ingiza wanzar da zaman lafiya, da goyon bayan tattaunawa.

A nasa ɓangaren, Xi Jinping ya jaddada cewa, abu mafi muhimmanci shi ne daƙile ƙara ƙazantar al’amura. Ya ce Sin na goyon bayan ƙasashen Faransa da Jamus, a fannin kafa tsarin daidaito, mai dacewa, kuma wanda zai wanzar da tsaron Turai bisa moriyar nahiyar.

Fassarawa: Saminu daga CRI Hausa