Daga BASHIR ISAH
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai shi ne zai shugabanci taron SAEMA karo na biyar da za a yi haɗe taron SCA karo na uku wanda zai gudana ranar Alhamis, 7 ga Disamban 2023.
Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar taron da aka yaɗa.
Sauran manyan jami’an da za su haskaka taron kamar yadda sanarwar ta nuna, sun haɗa da: Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Saha’anin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu; Shugaban NIPR, Dr. Ikeliaku; Babban Daraktan NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi da dai sauransu.
Taron wanda zai tattauna rawar da sadarwa ke takawa a fagen tsaron ƙasa, zai gudana ne ƙarƙashin shiryawar Image Merchants Promotion, IMPR, Limited; mawallafan jaridun PRNigeria da Economic Confidential da Politics Digest, da sauransu.
A cewar sanarwar, taron zai gudana ne a NICON Luxury da ke Abuja, inda Ministan Labarai, Alh. Idris zai kasance shugaban taro, yayin da NSA Ribadu a matsayin babban baƙo na musamman.
Malam Kashifu Inuwa ne ake sa ran ya gabatar da lacca kan taken taron, yayin da Shugaban NIPR, Dr. Neliaku zai kasance babban mai masaukin baƙi.
