Tsakanin Hisba da Hukumar Tace Finafinai: Ko tafiya tare zai kai su ga nasara?

Daga AISHA ASAS 

A kwanaki biyu baya, Hukumar Hisbah ta sasanta da masana’antar Kannywood, inda ta kai ga matsayar da za ta kawo zaman lafiya a tsakaninsu. 

Hukumar Hisbah ƙarƙashin jagorancin shehin malami, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ta ce, ba za ta ƙara tunkarar masu shirya finafinai kai tsaye ba kan wani abu na rashin dacewa da suka aikata, maimakon haka za ta waiwayi Hukumar Tace Finafinai wadda ita ce ke da alhakin kula da lamarin da ya shafi wannan ɓangaren. 

Hakan ya biyo bayan wani zama na musamman da hukumomin biyu suka yi tare da jagororin masana’antar Kannywood a ranar Talatar da ta gabata.

Maƙasudin wannan zama dai shi ne, samar da maslaha kan saɓanin da ya shiga tsakanin Hisbah da ‘yan fim a makon jiya, yayin da hukumar ta Hisbah ta gayyato wasu daga cikin su, gayyatar da suka ce ba su ji daɗin yadda aka yi masu ita ba.

Idan mai karatu yana bibiye da kafafen sadarwa, zai ga cewa, da yawa daga cikinsu sun tada jijiyoyin wuya kan wannan gayyata, inda kowanne daga cikinsu da irin nasa martani.

Baya ga haka, a ‘yan kwanakin baya ne aka samu wani jarumi kuma mawaƙi a masana’antar mai suna Abdallah Amdaz ya yi wani jawabi a gaban shugabannin hukumar ta Hisbah, waɗanda suka jawo ce-ce-kuce kuma wasu suke kallon kalaman nasa a matsayin tozarci gare su, kuma suke ganin bai cancanci Hisbah ta kira shi ba, a matsayinsa na wanda ba shugaba a Kannywood.

Sanadiyyar hakan ne shugabannin Kannywood da kuma Hukumar Tace Finafinai ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, suka yi zama da hukumar Hisbah, wanda zaman ya haifar da yarjejeniyar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da juna don ganin sun kawar da baɗalla da kuma duk wani abu da zai taɓa ƙimar addini da kuma al’adunmu.

Shugaban Hukumar Hisbah Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa na daga cikin waɗanda suka yijawabi a wannan zama, shi ma shugaban Hukumar Tace Finafinai Malam Abba El-Mustapha ya yi bayanin matsayin hukumar sa da kuma irin ƙoƙarin da ta ke yi na ganin ta kawo gyara a Kannywood tare da tsiratar da tarbiyya. 

Shugaban MOPPAN na qasa Dakta Sarari, ya tofa albarkacin bakinsa, sannan ɗaya daga cikin masu wakiltar Kannywood Malam Khalid Musa, shi ma ya yi nasa jawabin da aka yi wa taken ‘tsakanin malamai da ‘yan Kannywood’.

Daga ƙarshe an yi matsaya kan cewa, baya ga kauce ladabtar da ‘yan fim kai tsaye da hukumar Hisbah za ta yi, za a samar da wani tsari na fahimtar juna tsakanin Hisbah da kuma masu yin fim, har aka yi alqawarin shirya taro na kwana uku, wanda ɓangarorin uku, wato hukumar Hisbah, hukumar tace finafinai da kuma ita karan kanta masana’antar Kannywood za su halarta, da ƙudurin kyautata alaƙa da fahimtar juna. 

Da wannan ne muka je kan tambayar mu ta ko tafiya tare tsakanin hukumar Hisbah, hukumar tace finafinai da masana’antar Kannywood zai iya yiwa? Duba da cewa, ita hukumar Hisbah tana aikinta ne bisa ga tsari na addinin Islama, kuma kaso da yawa na ababen da ake yi a finafinai tana kallonsu a matsayin rashin dacewa. Ita kuwa masana’antar tana kallon ababe da dama da ta ke yi a matsayin tafiya da zamani ko mu ce cigaba. 

Idan muka yi duba da bambancin da ke tsakanin ɓangarorin, sai mu ga kamar abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa, sai dai idan muka waiwayi irin shiri da ayyukan da Hukumar Tace Finafinai ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha ta fara shimfiɗawa za mu iya cewa, hakan ba zai zama abin mamaki ba idan hukumomin biyu sun yi tafiya kafaɗa da kafaɗa ba, sakamakon nuni da suke yi na fatan da take da shi ga masa’antar kusan daidai yake da irin wanda hukumar Hisbah take da shi.

Idan muka ɗauki dakatar da jarumai har biyu da hukumar ta tace finafinai ta yi a ɗan lokacin nan a matsayin misali, za mu fahimci tafiyar ta da Hisbah mai yiwa ce. Duba da dalilan da suka sa aka dakatar da su. 

Abdulsahir, Malam Ali na cikin shirin ‘Kwana Casa’in’ shi ne hukumar ta fara dakatarwa, bayan ta kama shi da laifin yaɗa bidiyon batsa.

An ruwaito cewa, jarumin ya yi wani bidiyo a kafar Tiktok, inda yake maganganun da ba su dace ya yi ba.

Baya ga haka an tabbatar da cewa ya sha yin ababe na rashin ɗa’a, waɗanda hukumar ta ce, ta yi duba da su da kuma irin ƙorafe-ƙorafen da take samu kansa ne ta yanke masa hukuncin dakatar da shi tsayin shekaru biyu.

Sai kuma Khadija Kabir wadda aka fi sani da Khadija Mai numfashi, hukumar ta dakatar da ita sakamakon wata rawa ta rashin dacewa da ta yi a gidan gala. Rawar ta ƙazanta ta yadda wanda suke rawar a tare har yana tava jikinta, wanda hakan ko kaɗan bai dace da al’ada ta malam Bahaushe ba.

Sakamakon haka ne, shugaban hukumar Abba El-Mustapha ya sanar da cewa, an dakatar da ita na tsayin shekaru biyu, kuma ya yi kira ga duk wani mai aikin fim a ƙarƙashin masana’antar Kannywood da ya kauce wa saka ta fim ɗin sa.

Da wannan ne za mu iya cewa, fahimtar juna tare da aiki tare tsakanin hukumar Hisbah da Hukumar Tace Finafinai babbar hanyar samar da mafita ce kan yawaitar ayyukan rashin dacewa da ke tsakanin masu fim ko masu ƙoƙarin shiga harkar.