
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Tsaro, Christopher Musa ya sabunta tattaunawa akan tallafin Matar Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu ga masu sana’ar siyar da ƙosai da sauran ƙananan ‘yan kasuwa, inda ya ce mahaifiyarsa ta kasance mai tallafa wa gidansu ta sana’ar koko da ƙosai a lokacin tasowarsa.
Ya bayyana cewa, yana alfahari da aiki tuƙuru na mahaifiyar tasa ta sana’ar don haka bai dace wani ɗan Nijeriya ya riƙa yi wa masu ƙananan sana’o’i kallon ƙasƙanci ko kallon wasu ayyukan halaliya na marasa ƙarfi a matsayin ƙasƙantattu ba.
Kalaman ministan na zuwa ne bayan makonni da tallafin matar shugaban ƙasar ga masu siyar da ƙosai da wasu masu ƙananan sana’o’i ya tayar da hazo a sassan Nijeriya.
Janar Musa ya bayyana haka ne a wani taron horarwa da wayar da kai kan lamuran kuɗi na kwana guda ga zawarawa da matan aure da aka gudanar a Barikin Lungi da ke Birnin Tarayya Abuja a ƙarshen mako.
Ma’aikatar Tsaro da haɗin-gwiwar Hukumar kula da Ci-gaban Ƙanana da Matsakaitan ‘Yan kasuwa ta Ƙasa (SMEDAN) ne suka shirya taron wanda aka yi wa laƙabi da “Renewed Hope for Families of the Armed Forces of Nigeria through Entrepreneurship and Enterprise Development”, wato sabunta fata ga iyalan sojojin Nijeriya ta ci-gaban kasuwanci da ƙananan sana’o’i.
Da yake tsokaci kan kalaman da suka janyo cece-kuce na matar shugaban ƙasar wajen ƙarfafa wa masu ƙananan sana’o’i gwiwa, ministan tsaron ya bayar da kariya akan hakan wajen faɗar halin gidansu a lokacin da yake girma daga yaranta wajen nuna muhimmancin ƙananan sana’o’i ga kare mutuncin masu ƙaramin ƙarfi a lokacin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
A cewarsa, “tsayuwata a yau a matsayin ministan tsaro, sayar da kokon mahaifiyata ya taimaka. Wannan kokon ne ya tallafa wa mahaifiyata har na kai ga inda nake a yau. Ina alfahari da cewa mahaifiyata ta taimaka wa mahaifina ta silar siyar da ƙosai da akamu,” inji shi.
Kazalika, ministan ya ƙarfafa muhimmancin inganta rayuwar mata musamman iyalan sojoji ta hanyar koya musu aikin hannu da ci-gaban ƙananan kasuwanci a matsayin hanyar bunƙasa ƙarfin tattalin arziƙinsu.
