Ministocin harkokin wajen Sin da Zambiya sun tattauna a Anhui

Daga CMG HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, a ranar Asabar ya tattauna da ministan harkokin wajen ƙasar Zambia, Stanley Kasongo Kakubo, a birnin Tunxi na lardin Anhui dake gabashin ƙasar Sin.

Da yake maraba da Kakubo, a matsayin ministan harkokin waje na farko na ƙasar da ke kudu da hamadar Afrika da ya ziyarci ƙasar Sin tun bayan ɓarkewar annobar COVID-19, Wang ya ce, ƙasar Sin tana goyon bayan zabin da ƙasar Zambia take da shi na neman hanyar ci gabanta wadda ta dace da yanayinta.

Wang ya ƙara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Zambia domin ƙarfafa tuntubar juna, da zurfafa musayar ƙwarewar gwamnatocin biyu, da kyautata mu’amala da kuma faɗaɗa hadin gwiwar ƙasashen a fannoni daban-daban.

Kakubo, ya taya ƙasar Sin murnar samun nasarar karɓar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022, sannan ya yaba wa ƙasar Sin bisa gudunmawar da take baiwa ci gaban nahiyar Afrika cikin dogon lokaci, da kuma yadda take kiyaye dokoki da tabbatar da adalci a harkokin ƙasa da ƙasa.

Ɓangarorin biyu, sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan batun Ukraine. Kakubo ya yabawa ƙasar Sin bisa rawar da take takawa wajen ƙara azama kan tattaunawar zaman lafiya, da kuma rawar da take takawa cikin dogon lokacin don tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.

Fassarawa: Ahmad