
Ɗaya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC kuma masanin tattali, Mohammed Hayatu-Deen, ya sanar da cewa ba zai halarci taron bayyana sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ba saboda zargin maguɗin zaɓe.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Hayatu-Deen ya bayyana damuwarsa kan yadda aka gudanar da zaɓen, yana mai cewa ya samu rahotannin maguɗi daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya ce, har yanzu yana tuntuɓar masu ba shi shawara domin yanke hukunci kan matakin da zai ɗauka na gaba.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na kan gaba a sakamakon farko daga jihohi da dama ciki har da Sokoto, Gombe, Yobe, Imo da Abia, yayin da Rotimi Amaechi ya samu nasara a Bayelsa.
Lamarin na zuwa ne yayin da jam’iyyar ADC ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinta a ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen 2027.
