
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Borno ta sanar da sanya takunkumin zirga-zirgar ababen hawa da mutane na wucin-gadi domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da sallar Idi a gobe Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa, takunkumin, wanda Gwamna Babagana Zulum ya amince da shi, zai fara aiki ne daga ƙarfe 6 na safe zuwa 11 na safe a ranar Laraba. Haka kuma, zai shafi motoci, adaidaita sahu da babura.
Matakin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Rundunar Sojin Nijeriya ta yi gargaɗin yiwuwar hare-haren ta’addanci a wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar.
A sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Tsaron Cikin Gida, Usman Tar ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne domin ƙara inganta tsaro a yayin bikin sallah da al’umma ke gudanar da shungulla.
Ya yi kira ga mazauna jihar da su gudanar da sallah a filayen Idi mafi kusa da gidajensu domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen tantance jama’a cikin sauki.
A cewar sanarwar, jami’an tsaro, motocin ɗaukar marasa lafiya, jami’an kashe gobara da sauran ma’aikatan da ke gudanar da muhimman ayyuka tare da sahihin katin shaida, takunkumin bai shafe su ba.
