Gombe: Fusataccen mai neman takarar gwamna a PDP ya ƙi amincewa da Pantami

Spread the love

Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan a Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya yi watsi da sanarwar da ta bayyana tsohon Ministan Sadarwa Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamna a PDP a zaɓen 2027.

Saleh ya bayyana wannan mataki a matsayin wanda bai dace ba, yana mai cewa ba a bi ka’idojin jam’iyya yadda ya kamata ba wajen gudanar da zaben fidda gwani da ya haifar da nasarar Pantami.

Ya ce, shigar Pantami cikin takarar PDP ya keta dokokin cikin gida na jam’iyya tare da tauye haƙƙin sauran ‘yan takara da suka fara takara tun farko.

Ya kuma zargi Pantami da cin moriyar abin da ya kira “rashin adalci a PDP” duk da cewa Pantami ya taɓa koka wa cewa ya fuskanci rashin adalci a tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.

Hamma Saleh ya ce abin mamaki ne yadda mutum zai yi korafi kan rashin adalci a wata jam’iyya sannan ya aikata irin wannan a wata jam’iyyar daban, yana mai cewa hakan na barazana ga dimokiraɗiyyar cikin gida a PDP.

Ya sanar da cewa zai ɗauki matakin shari’a domin kalubalantar sahihancin bayyana Pantami a matsayin ɗan takara, yana mai cewa dole a bi doka domin kare tsarin zaben jam’iyya.

A ƙarshe, Saleh ya jaddada cewa zai cigaba da neman adalci tare da kira ga shugabannin PDP da su tabbatar da gaskiya, bin doka, da kare tsarin dimukraɗiyyar cikin jam’iyya domin kare martabarta.

By Babaji