Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Kwanci tashi ba wuya ga mai yawan rai. Idan Allah ya kai mu gobe Asabar cikin rayayyu, ’yan Nijeriya miliyan 93 da dubu ɗari 5 ake sa ran za su fita su kaɗa ƙuri’unsu a rumfunan zaɓe 176,606 a dukkan faɗin ƙasar nan. Kamar yadda muke sane wannan zave da za a yi ya shafi matakin ƙasa ne, wato Shugaban Ƙasa, Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya, da kujerar Ɗan Majalisar Dattijai. Yayin da zaɓe na gaba zai shafi kujerar Gwamna, da ’Yan Majalisar Jihohi.
Wani batu mai muhimmanci da ya ke ɗaukar hankalin ’yan Nijeriya musamman ’yan siyasa da masu hidimar zaɓe da suka haɗa da Hukumar Zaɓe ta INEC shi ne batun sayen ƙuri’a, wato yadda ’yan siyasa ke bai wa masu zaɓe wani abin hasafi don su zaɓi ɗan takarar da suke goyon baya. Wannan wani abu ne da ya daɗe yana faruwa a siyasar Nijeriya, inda ake samun wasu da kan je cibiyar zaɓe da ganye a kansu, suna jiran wanda zai ba su kuɗi, su zaɓi dan takarar da yake so.
Ba damuwar su ’yanci ko cancantar wanda za su zaɓa ba, matuƙar miyar gidan su za ta yi ja. Irin wannan ta sha faruwa ba tun yanzu ba, yayin da gwamnati da masu faɗa a ji ke ta wayar da kan jama’a, kan illar sayar da ’yanci ko sayar da ƙuri’a. Amma har yanzu ba ta canja zani ba, duk kuwa da yadda za ka ji jama’a na ta muhawara da kumfar baki a kan ɗan takarar da suke so. A kan maggi ko ashana, gishirin miya ko taliya, sai a canzawa mutum ra’ayi.
Abin da dama ke ganin kuskure ne, yanzu ya fara zama al’adar lokacin zaɓe ko halayyar ’yan siyasa, har ma ji za ka yi ana cewa a fito da kayan aiki a je neman goyon bayan jama’a. Wasu kuma na cewa, duk ɗan takarar da bai ba su wani abu ba, ba za su zaɓe shi ba.
Wani lokaci ma har malamai da ’yan siyasa za ka ji suna cewa, idan an ba ku kuɗi ku karva, amma ku zaɓi wanda ku ke so! A wajen su amfani da kuɗi a siyasa daidai ne, ko da kuwa kuɗin na sata ne ko, haƙƙin talakawan ne dama aka ɓoye sai zaɓe ya gabato a fito da kuɗin ana ɗan yaga musu wani abu da ko cefanen gidan su ba zai ishe su ba.
Ba abin mamaki ba ne ka ji matasa sun zauna a teburin mai shayi ko a majalisa, suna musun wanne ɗan takara ne ya fi kuɗi ko ya fi yawan rabawa mutane kuɗi da kayayyakin sayen ra’ayin jama’a. Har ma ka ji ana kashe gwiwar magoya bayan wani ɗan takara komai cancantarsa, saboda ba shi da kuɗi ko baya rabar da kuɗi, a riƙa cewa babu inda zai je, don ba shi da kuɗi. Suna yi wa hidimar siyasa kallon, iya kuɗin ka iya shagalinka!
Adolphus Wabara tsohon shugaban Majalisar Dattijai ya tava faɗin cewa, siyasar Nijeriya kamar kasuwanci take. ’Yan siyasa na zuba jarin su ne da duk wani abu da suka mallaka, don suna sa rai da idan mulki ya zo hannunsu za su samu gwaggwavar riba ninkin abin da suka kashe a lokacin yaƙin neman zave. Lokacin kallon cancanta, ilimi, gogewa, gaskiya da riƙon amanar ɗan takara, wajen auna dacewar zaɓen ɗan takara ta wuce.
Me muka samu a jikinka shi ne magana, ko kuma wanne kusanci muke da kai don idan ka ci mu riƙa zagayowa kana kashe mana wutar gaban mu, ko da kuwa ba ka taimakawa cigaban yankin ka ba, ko taimakawa marasa jari da masu ƙananan sana’o’i da marasa ayyukan yi ba.
Zaɓe a Nijeriya ya zama wata babbar harka da ke buƙatar maƙudan kuɗaɗe, don gudanar da hidimar yaƙin neman zaɓe, ɗaukar nauyin kaiwa da komowar abokan aiki masu taya ayyuka, ƙungiyoyin mata da matasa da za su yi ta zarya suna nuna goyon baya, da ’yan shaye-shaye masu ɗaukar sanduna da gariyo suna bin ɗan takara ana iface-iface a titi da cikin anguwanni, ɗaukar nauyin motoci da zuba mai.
Tallafawa iyayen jam’iyya, buɗe ofisoshin yaƙin neman zaɓe, buga fostoci manya da ƙanana, sayen kayan rabawa jama’a da shugabannin al’umma, malaman addini da sarakuna, don neman haɗin kansu, kafin a zo kan sayen ƙuri’a ko ra’ayin masu zaɓe, da biyan wakilan da za su sa ido a kan zaɓen da za a gudanar. Idan mutum ya yi lissafi zai ga lallai, ba qaramin mai kuɗi ne zai iya jurewa yaƙin neman zaɓe ko shiga takara ba.
Irin wannan tsarin siyasar da muke ciki, shi ne yake hana nagartattun mutane, waɗanda suka fi dacewa da cancanta shiga harkokin siyasa domin ba su da kuɗin da za su yi facaka da su ko su sayi ra’ayin jama’a. Su kuma ruɓaɓɓun ’yan siyasar da ke ta kaiwa da komowa suna karakaina a tsakanin mu, sun san ba cancantar su ce da halayen su nagari ya sa ake ƙaunar su ba, kuɗin su da kyaututtukan da suke yi ne suka saya musu wannan farin jinin har wasu ke ganin idan ba su aka zaɓa ba sai dai a yi mutuwar kasko, ko a zubar da jini.
Sun gane cewa halin takurar da jama’a ke ciki ita ce ta sa ko me suka faɗa haka za a bi su kuma a so su, saboda kwaɗayin abin da za su raba, wanda su talakawa dama a matse suke su samu. Da gangan wani lokaci ’yan siyasa ke azabtar da mutane da talauci da yunwa, domin su zama su ne kaɗai mafuskantar da za a je neman tsira, yayin da su kuma za su shimfiɗa tsari na bautarwa da wulaƙanta jama’a, sai abin da suka fito da shi suka bayar.
Sai ka ga an fito da mudun shinkafa biyu ana raba wa mutane, ko fallen zani ana ba mata, amma sai a riƙa nuna wa duniya cewa, buhun shinkafa da turamen atamfa ake rabawa. Wani wajen ma sunƙin taliya ce ƙwaya ɗaya za a bayar da ƙullin gishiri a matsayin an raba katan-katan ɗin kayan masarufi.
Idan kuwa kuɗi ne haka a wulaƙance za ka ga ana miƙa wa mutane Naira ɗari biyu ko ɗari ɗaya, a ƙauyuka ma har hamsin hamsin ake bayarwa wai na sayen ƙuri’a. Idan ka ga an sayi ƙuri’a a Naira ɗari 5 to, wataƙila a birni ne. In ka bibiya daga sama shi uban gayyar ya ba da dubu biyu ne ko dubu ɗaya, amma kafin abin ya kai ga talaka an zabtare sauran.
Wani bidiyo da na gani ya nuna yadda ’yan siyasa a wata Jam’iyya suka haɗa mata wai za a basu tallafi, ashe ɗan ƙunshin lemon kwalba da wasu tarkace ne aka ƙulle a leda ana wurga musu suna rububi a kansa, wai wannan shi ne tallafi, da tausayawa mata.
A nan ne har aka samu wasu wayayyu daga cikin matan da suke ganin hakan bai dace ba suka yi bore. Abin tausayi abin takaici, haka ’yan siyasa ke amfani da talaucin mutane suna wofintar da su, wai suna nuna su ne masu ƙaunarsu.
Duk da kasancewar kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokar zaɓe sun haramta amfani da kuɗi ko wata kadara wajen sayen ƙuri’a ko canja ra’ayin mutane kan abin da suke so, amma sam ’yan siyasar ƙasar nan ba ruwan su da wannan, har ma ƙorafi da surutai suke yi na an shigo da tsarin rage mu’amala da tsabar kuɗi da sauya launin Naira da aka yi a wannan lokaci ne, don a hana su cin zave.
A wannan maganar har da gwamnoni waɗanda su ne ma a sahun gaba suna kai ƙarar gwamnatin tarayya, don kotu ta matsa wa gwamnati lamba a ƙara ɗaga lokacin amfani da tsohon kuɗi, don su fito da kuɗaɗen da suka tanada na sayen ƙuri’a, a raba wa jama’a. Babu ma kamar yadda yanzu rayuwar talaka ta shiga ƙaƙa ni kayi, saboda rashin kuɗin da zai riqe ko zai sarrafa a hannu don kula da buƙatun iyali.
Na ga wani bidiyo da ke yawo a wayoyin mutane inda wakilan wata jam’iyya suka fito da sabbabbin kuɗi, ’yan ɗari bibbiyu suna kasafta yadda za a rabawa mutane, masu katin zaɓe a hannu. Abin haushi da takaici da Naira ɗari 2 za a sayi ƙuri’ar talaka, ya sake shafe wasu shekaru 4 cikin ƙunci da talauci. Kamar yadda na faɗa a baya su waɗannan wakilan da ake bai wa kuɗi su sayi ƙuri’a a hannun talakawa don su zaɓi wani ɗan takara, sai sun yagi nasu kason kafin su yaga wa na kasa ɗari-ɗari ko hamsin-hamsin.
Ya kamata talakan ƙasar nan ya gane cewa, yadda ’yan siyasar nan ke rububin neman ƙuri’ar sa ƙwaya ɗayan nan to, babu shakka lallai tana da daraja ne, kuma ita ce abin gadararsa da tinƙahonsa, a matsayin sa na ɗan ƙasa. Kada mu bari a sayi ’yancin mu da gwangwanin suga ko sunqin taliya. A riƙa yi mana kallon matsiyata, almajirai. Mu yi amfani da damar da muke da ita mu zaɓi ’yan takarar da muke sa ran za su yi mana abin kirki, za su yi ƙoƙarin kawo sauye-sauye da cigaba da kowa zai yi murna da mulkin dimukuraɗiyya.
Wasu na nan gobe za su lave suna jiran ku fito rumfunan zaɓe su kuma su biyo ku da canjin sabon kuɗi, don su sayi ’yancin ku da ra’ayinku, zuwa ga wani xan takarar da ba shi ku ke ra’ayi ba, amma saboda matsuwa a da takura haka wasun mu za su karɓa, suna ji suna gani, saboda babu yadda suka iya. Mu yi haƙuri mu danne kwaɗayinmu da takurar da mu ke ciki ta neman sabon kuɗi ko canjin abin yin cefane, mu fita mu yi zaɓe yadda ya dace ga waɗanda suka cancanta, ko ba su samu nasara ba Allah ya gani ka ba da gudunmawa don ganin an zaɓi nagari an yi gaskiya da adalci.
Mu gayawa masu bibiyar mu da kuɗi da abin masarufi cewa yanzu mun waye ba za mu karɓi abin da suke ƙoƙarin sayen mu da shi ba, ƙuri’ar mu ba ta sayarwa ba ce!
