Mulki da sha’aninsa

Manhaja logo

Daga MUHAMMAD MAHMUD MUSTAPHA

Himma ba ta ga rago! Malam Ali Zarnuji na cewa a Ta’alimi, “ma’abota himma ne kawai ke samun manya-manyan matsayai a duniya da lahira.” Babu abinda Allah ba ya bayarwa a dalilin himma in ji ma’abota hikima. Imam al-Gazali a Sirrul Alamina yana cewa: “maɗaukakiyar himma kan sanya mutum ya samu har abinda bai cancanci ya samu ba a zahiri”.

Almajirai, talakawa, bayi da ‘ya’yansu da yawa sun zama manyan sarakuna da shugabanni saboda maɗaukakiyar himmar da suka samu daga baya. Mahaifin Zulƙarnaini, Sarkin duniya, inji masu tarihi, masaƙi ne. Zulƙarnaini a maraya ya taso. An ce yana ɗan mitsitsin yaro mahaifiyarsa ta kai shi makarantar koyar da sana’o’i a birnin Istanbul.

Da ta nemi ya zavi sana’ar da yake son yi a rayuwarsa don ya fara koya tun kafin ya girma, ga mamakinta, a saboda ɗaukakar himmarsa, sai ya zaɓi kambin sarauta wanda ke a sanye a kan gingimemen gunkin wani sarki a makarantar. Ta-yi-ta-yi ta kawar da hannunsa ko zai zaɓi wani abin, amma ya ƙi. Wannan ya sanya masu neman shugabanci ba su da maƙamin da ya wuce himma; da ita ne suke cimma komai, da ita ne suke cimma burikansu.

Sai dai a maganar shugabanci a iya cewa, ba hawan ba, saukar; ba ɗaukar nauyin ba, iya sauke haƙƙin. Domin Annabi SAW yana cewa: “shugaba marar adalci shi ya fi shan tsananin azaba ranar alƙiyama”. A ƙarin wasu Hadisai masu yawa da Malam Munziri ya kawo a Attargibu wattarhibu sun bayyana cewa Allah SWT yana fushi da azzalumin shugaba, ba ya karvar sallarsa, ba ya karɓar kalmar shahadarsa (cikakkiyar karva), kuma Annabi SAW ba zai cece shi ba.

Haka kuma zaluncin azzaluman shugabanni yana kawo fari da talauci a cikin jama’a. Wasu hadisan kuma su na nuna cewa azzaluman shugabanni su ne farkon shiga gidan wuta. Ga kuma tsinuwar Annabi (Rayuwata fansa ce a gare shi) ga azzaluman shugabanni, da kuma shugabanni masu naɗa wakilai da bayar da kujeru da mukamai saboda san rai ko rashawa. A wani Hadisin ma Annabi SAW cewa yake: “duk shugaban da ya yi wa jama’arsa rufa-rufa ya cuce su a wani abu to kuwa Allah ya haramta masa shiga Aljanna”.

Idan kuwa shugaba ya yi adalci a mulkinsa to Hadisan Annabi SAW masu yawa suna yi masa bisharar shan daɗin inuwar Allah a ranar da  ko ina zafi ne da wahala, Allah ba zai taba wofuntar da addu’o’insa ba, za a girmama shi a gaban jama’a, a aza shi bisa gadon girma na haske, darajar yini guda a rayuwarsa dai-dai take da ibadar wasu ta shekaru sittin. Shugaba mai adalci shi Allah ya fi so a ranar Alƙiyama. Wata Rana Sayyiduna Abu Zarrin Al-Gifari ya tambayi Annabi SAW ya Manzon Allah me ne ne a rubuce cikin litattafan Annabi Ibrahim AS?

Sai Annabi ya ce da shi: karin magana ne da azancin zance gaba ɗaya a cikinsu. [Ana cewa a cikinsu] kai shugaba sarkin ruɗuwa da mulkinsa, Ni ban tura ka shugabanci dan ka tara wa kanka duniya wata a kan wata ba, na tura ka ne saboda ka amsa kiran mutanen da aka zalunta, ko da kuwa ba su da imani. Shugaba a ɗaɗɗaure yake da sasari, babu abinda zai kwance shi ya bashi yanci sai adalci.

Adalci shi ne aza komai a inda ya dace. Babu mutumin da zai samu shugabanci ya iya yin adalci sai idan yana da siffofi irin na nagartattun jagorori. Siffofi biyar ne. Ta farko mutum ya zama ƙwaƙƙwara, abinda Malam Mawardi a al-Ahkamus Suldaniyyah ya fassara da jarumin mutum mai lafiyar gavvai da majiya motsi. Na biyu mutum ya zamanto mai kima da martaba a idon mutane, kada ya zama mai aikata ayyukan ƙasƙanci, sharholiya ko bayyana laifuffuka.

Malam Mawardi adala kawai ya kira wannan siffar. Na uku amini , mutane sun yadda da shi a dukiyarsu da baki ɗayan rayuwarsu; ba zai ci amanarsu ba. Na hudu Hafizi , mai iya kiyaye rawukan mutane, lafiyarsu, dukiyoyinsu, mutuncinsu da tsare-tsaren rayuwarsu; zai iya kiyaye su daga sharrin kansa, zai iya kiyaye su daga sharrin waninsa. Na ƙarshe alimi , masani amma ba na wa’azi ba, masani na dabarbaru da hanyoyin gudanar da shugabanci. Haramun ne a baiwa marar waɗannan siffofi shugabanci, haramun ne ya naima. Annabi SAW ya hana Abdullahi ɗan Samurata, ya hana Abu Zarrin al-Gifari, naiman shugabanci, saboda gudun taɓewa, nadama da hawa kujera ba tare da cancanta ba.

Malamai sun fahimto waɗannan siffofi ne na wanda ya cancanci zamowa shugaba daga ayoyi guda biyu a cikin al-Ƙur’ani. Ta farko shaidar da ‘yar Annabi Shu’aibu ta bayar a kan Annabi Musa: “baba ka ɗauke shi aiki domin alkhairin da yake a tare da shi in ka ɗauke shin; kasancewarsa ƙwaƙƙwara kuma amintacce”. Aya ta biyu kuma ganawar da ta kasance tsakanin Annabi Yusuf da Sarkin Misra: “yayin da (Sarkin Misra) yayi magana da shi (Annabi Yusuf) sai ya ce daga yau (Yusufu) kai mai matsayi ne kuma amintacce a wajenmu. Sai (Annabi Yusuf) ya ce sanya ni na kula da taskokin qasa domin ni mai iya kiyaye su ne kuma masanin hanyoyin gudanar da su ne.

Sharaɗin shugabanci ke nan. Nasarar gudanar da shi kuma fa?! A musulunce sai shugaba ya lura da lamurra biyar. Na farko manufar shugabancinsa ta zamanto ta rahama ce domin samarwa al’umma jin daɗi, walwala da sauqin rayuwa. Tsare-tsarensa sa iya zuwa da matsi, runtsi, raɗaɗi ko wahala a wasu lokutan, amma saboda manufarsa a haƙiƙa jin ƙai ce za su zam tamkar magani mai ɗaci ko fiɗa ta likita. Na biyu ya zama mai afuwa. Na uku ya yawaita yi wa al’ummarsa kyakkyawar addu’a musamman a lokuta na tsakar dare da bayan salloli. Fiyayyun shugabanni su ne waɗanda suke muku addu’a kuke musu addu’a – inji Hadisin Annabi SAW. Hakan zai haifar da wata ƙauna da tsananin soyayya ta musamman a tsakanin shugabanni da mabiya.

Na huɗu shawara da ma’abota hankali da cancanta kafin zartar da kowane hukunci. Na biyar da zarar an yanke hukunci, to babu mi’ara-koma-baya, sai dogaro da Allah kawai da zartarwa; hakan zai kiyaye daraja da kwarjinin mulkin.

Duk waɗannan abubuwa suna nan a inda Allah SWT yake cewa da Annabinsa SAW: “a saboda rahmar dake zuwar ma daga Allah ka tausasa a gare su, da ka kasance mai kaushin hali da ƙeƙasar zuciya da tuni sun watse daga wajenka, saboda haka ka yi musu afuwa, ka naima musu gafara kuma ka naimi shawarwarinsu a lamura, duk lokacin da ka yunƙura kuma to ka dogara da Allah.

Wajibi ne mutane su samu shugaba wanda zai kula da maslahohinsu – ko da kuwa a ce mutum uku ne kacal a dokar daji. Shugaban Azhar Imam Ahmad al-Dayyib yana cewa: “shugabanni a yanzu su ne Sarakunan Dauloli da Shugabannin Ƙasashe, Gwamnoninsu, Ministocinsu, Wakilansu da Mataimakansu.

Saboda haka a bada himma a naimi mulki da ɗaukaka. Daidai ne. Daga an yi kira sai a ji  kana ko ma kina: himma dai ɗan shehu! Sai dai a kyautata niyya a tuna da hikmar Malam Ibnu Ada’illahi a Hikamu da ya ke cewa: “kada niyyar himmarka [ta samun komai a duniya da lahira] ta ƙetare ta tafi naiman yaddar wanin Allah. Allah dai ya tsare kada harshen lahira ya dinga cewa da shugabannin zamani a yau: yaro bari murna karenka ya kama kura!