Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL) ya bayyana cin ribar Naira biliyan 502 a watan Nuwamba 2025, duk da raguwar samar da ɗanyen mai a watan.
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin na gwamnati ya shiga gasar rage farashin man fetur a kasuwar, inda ya rage farashin litar man zuwa ƙasa da N800.
Rahoton kuɗi da ayyukan NNPC na watan Nuwamba 2025, wanda aka fitar a ranar Laraba, ya nuna cewa kamfanin ya samu kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 4.36 a cikin watan, wanda ya ɗan ɗara na watan Oktoba.
An danganta wannan kyakkyawan sakamako da ƙaruwar samar da iskar gas, samun damar amfani da bututun mai gaba ɗaya, da kuma daidaitaccen samar da man cikin gida, wanda ya taimaka wajen rage tasirin matsalolin samar da ɗanyen mai.
Samar da ɗanyen mai ya kai matsakaicin ganga miliyan 1.36 a rana a watan Nuwamba, ya ɗan fi na ganga miliyan 1.30 da aka samu a Oktoba, amma har yanzu bai kai ƙololuwar ganga miliyan 1.77 da aka samu a farkon shekarar 2025 ba.
Wannan ya nuna fara farfaɗowa bayan watanni uku na raguwar samarwa daga watan Agusta zuwa Oktoba.
NNPCL ya ce ribar N502bn da aka samu a watan ta samo asali ne daga ƙaruwa a samar da gas, ƙaruwar ciniki, da kuma samun damar amfani da kayayyakin more rayuwa, duk da matsalolin da ake fuskanta a wasu wuraren samar da ɗanyen man.
Jimillar kuɗaɗen da aka biya zuwa Asusun Gwamnatin Tarayya ya kai Naira tiriliyan 12.12 daga watan Janairu zuwa Oktoba 2025, wanda ya nuna ƙarin gudunmawar NNPC ga kuɗaɗen gwamnati a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.
A ɓangaren farashin fetur, NNPC ta rage farashin litar fetur zuwa ƙasa da N800, bayan an fara samun gasa daga masana’antar ɗangote, wadda ta rage farashin daga N828 zuwa N699 a lita.
Rahotanni sun nuna cewa, wasu gidajen mai na kamfanin NNPC a jihohin Legas da Ogun sun fara sayar da fetur a N785 a lita, domin yin gogayya da gidajen mai na ’yan kasuwa.
