Mun fara gudanar da harkokin karatu gadan-gadan a zango na 2025 a NSUK – Kwamared Jafar Abubakar

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Sabon mai magana da yawun babbar jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi (NSUK), Kwamared Jafar Abubakar ya ce tuni jami’ar ta fara aiwatar da harkokin karatu na zangon karatun sabuwar shekarar 2025 da ake ciki.

Kwamared Jafar Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa dake jami’ar ranar Litinin na mako da ake ciki.

Ya buƙaci ɗaliban babbar jami’ar mallakar gwamnatin jihar ta Nasarawa musamman wadanda basu dawo daga hutun karshen shekara da aka tafi kwanakin baya ba su hanzarta yin haka don a yanzu harkokin taratun yama yi nisa.

Kwamared Jafar Abubakar yace anata bangaren tuni hukumar gudanarwar jami’ar ta jajanta kudirin ta na cigaba da aiki tukuru wajen tabbatar ta bai wa daliban ingantaccen ilimin addini dana zamani don cimma muradun nata musamman a karkashen jagorancin shugabar ta farfesa Sas’adatu Hassan Liman.

Ga ɗaliban da a yanzu haka suka riga suka koma karatu a jami’ar Jafar Abubakar ya bukace su su mai da hankalin su kacokan ga harkokin karatun su su kuma guje wa duk wata dabi’a da ka iya jawo musu cikas a tafiyar tasu don a cewar sa mahukuntan jami’ar baza su yi wata-wata ba wajen cigaba da dau kwararan matakan hukunci akan duk wanda aka kama yana karya dokokin jami’ar batare da yin la’akari da matsayin sa ko na iyayen sa ba.

Dangane da batun zaɓen shugabannin daliban jami’ar da akafi sani da S.U.G election wadda aka gudanar kafin hutun shekarar da ta gabata 2025 wadda aka samu matsala akarshen zaben kwamarede Jafar Abubakar ya bayyana cewa mahukuntan jami’ar tuni suka yanke shawarar sake shirya tareda sanar da sabon ranar da za a gudanar da zaben nan bada dadewa ba inda ya gargadi daliban su cigaba da kwantar da hankalin su su kuma tabbatar suna kiyaye dokokin jami’ar musamman wadanda suka shafi zaben kafin lokaci da kuma bayan zaben inda akarshe ya taya ɗaliban bakiɗaya murnar ganin sabuwar shekarar 2025 a madadin hukumar gudanarwar jami’ar bakiɗaya.