Wata biyu kan karaga: Al’ummar Keffi na ci gaba da yaba wa Dokta Idris Damagani

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

A yanzu haka al’ummar ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa suna cigaba da yaba wa sabon shugabansu wanda aka zaɓa aka kuma rantsar kimanin watanni 2 kacal da suka gabata a inuwar jami’iyyar APC mai mulki a jihar wato Dokta Idris Ahmad Damagani dangane da tsalon shugabancin sa wadda acewar su ke cigaba da canja fatsalin karamar hukumar ta Keffi da kewayen ta baki daya kawo yanzu bayan watannin 2 kacal.

Waɗannan al’umma ainihin ‘yan karamar hukumar ta Keffi da wakilin mu ya zanta dasu game da ayyuka da salon shugabancin sabon shugaban nasu na yanzu dokta Idris Ahmad Damagani duk sun bayyana suka kuma sanar cewa tabbas sabon jagoran nasu matashin a yanzu haka yana cigaba da wuce samani da akayi masa a baya inda yana cigaba da kirkiro tareda da aiwatar da wasu dinbin ayukan cigaba a birnin na Keffi da kewayen ta baki daya da suka hada da samar musu da tsaptaceccen ruwan sha da asibitoti da gyarar hanyoyi da gina sabbi da kiwon lafiya da uwa uba tabbatar da tsaron yankunan da sauran su tunda ya hau karagar mulkin.

Sun ce da zuwan sabon shugaban ƙaramar hukumar ta Keffi kujerar bai bata lokaci ba inda ya fara zama da rukunin hukumomi dabandaban da al’ummar jihar ciki harda na jami’an tsaro don jin ra’ayoyin su da kalubalan da suke fuskanta a yankunan su inda nantake bada jimawa ba ya fara fit da sabbin tsare-tsare tareda aiwatar dasu da hakan acewar su tabbas yana cigaba da aifar da ƙa mai ido a fannin cigaba a duka matakai a karamar hukumar kawo yanzu.

Dangane da batun yawan hadura da suke faruwa a wani babban mahaden hanya (round about) dake cikin birnin na Keffi da dadewa al’ummar karamar hukumar ta Keffi da aka zanta dasu sun, sun bayyana cewa dazuwar sabon shugaban nasu dokta Idris Ahmad Damagani abu na farko daya fara aiwatar shine jimkadan bayan ya kai wani ziyara na musamman inda haduran ke yawan faruwa dake cigaba da jawo asaran rayuka da dukiyoyi da dama sai ya tuntubi gwamnatin jihar inda a yanzu haka suka shiga wata yarjejeniya ta musamman da karamar hukumar don fara aiwatar da wata aiki na musamman a wajen don rage ko kawo karshen lamarin kwata-kwata.

Sun kuma kara da cewa matashin kasancewa shima matashi ne dake tasowa yasan matsalolin matasa ‘yan uwan sa da sauran al’umma baki daya da hakan yasa a yanzu haka yana ta gudanar da ingantattun sabbin shirye-shirye dake cigaba da tallafa wa dinbin matasan karamar hukumar ciki harda mata da yara musamman a fannin ilimin su da sauran su batare da yin la’akari da banbancin siyasa, addini ko kabilanci ba.

Daga nan sai suka yi amfani da damar inda suka yi kira na musamman ga sauran al’ummar ƙaramar hukumar ta Keffi da kewayenta bakiɗaya su cigaba da bai wa matashin shugaban nasu Dokta Idris Ahmad Damagani cikakken goyon baya musamman ta kasancewa al’umma nagari masu bin dokokin zaman lafiya da saraunsu don bai wa shugaban damar cigaba da samar musu da ribobin dimokaraɗiyya a duka matakai kamar yadda yake yi a yanzu kana suka buƙace shi shi ma (shugaban su) ya cigada da kyawawan ayyukan cigaban.