Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Hon Sulaiman Muhammad Chamba, Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙaramar Hukumar Fagge ya ce an tantance ‘yan takarar neman tsayawa shugaban ƙaramar hukumar Fagge guda 25 amma daga baya aka yi maslaha aka fitar da mutum uku, ɗaya ya zama ɗan takara ɗaya mataimaki ɗaya zai zama sakatare, hakan ya samu ne kuwa saboda sun yarda duk ɗaya suke wanda Allah ya bai wa za a bi shi.
Ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce komai an yi shi ne a buɗe ba a boɓe ba da kowane ɗan takara yasan duk abinda aka yi ba a tsaye masa haƙƙi ba an yi lafiya an gama lafiya.
Ya ce nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu na fitar da gwanin ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Fagge da kansiloli na mazaɓun yankin an gudanar bisa doron gaskiya da baiwa kowa damarsa. An tantance da masalaha a tsakanin ‘yan takaran a yayin da suke tare wajen fitar da gwanin ba wata matsala a tsakanin su sai fahimta da girmama juna da sanin yakamata dattaku da suka nuna.
Hon.Sule Chamba ya ƙara da cewa yadda akayi masalaha a tsayar da ɗan takarar na shugaban ƙaramar hukumar haka aka yi na kansiloli na mazaɓu ba wanda aka tirsasa sai dai masalaha har daga baya ma kuɗaɗe da aka karɓa a hannun ‘yan takarar masu neman tsayawa shugaban ƙaramar hukuma da na kansiloli duk mayar musu aka yi a Fagge.
Tsohon zaɓaɓɓren shugaban ƙaramar hukumar na Fagge Sule Chamba ya tabbatar da cewa da su ‘yan takarar da su shugabannin jam’iyyar NNPP sun yarda duk ɗaya suke duk wanda Allah ya baiwa za a bi shi, akan haka ake kuma za su yi nasara a zaɓe mai zuwa da yardar Allah saboda irin kyakkyawar niyya ta jam’iyyar su ta NNPP.
Chamba ya ce wanda ya samu nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar na Fagge Hon. Salisu Usman Masu mutum ne mai ƙoƙari da ƙwazo domin a shekara ta 2003 sun yi takara da shi a matsayin mataimakinsa ba shi takara da aka yi yanzu za a yi mamaki domin yana da ɗabi’u masu kyau da zai kawo gyara da cigaba domin ɗan siyasa ne na ƙwarai daga tushe.
