Mun sasanta ma’aurata 3,579 a Jigawa – Hisbah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa ta ce ta sasanta ma’aurata 3,579 a 2021, kamar yadda Kwamnadan ta na jihar, Ibrahim Ɗahiru ya bayyana.

Ɗahiru ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN, a Dutse a Alhamis da ta gabata.

Kwamnadan ya yi bayanin cewa haƙƙin hukumar ne ta sasanta ma’aurata.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta sasanta tsakanin ‘yan kasuwa 41, iyaye da ‘ya’yn su 221, maƙwabta 319 da manoma da makiyaya 71.

“Sasanta tsakanin al’umma abu ne mai amfani da ya ke wanzar da soyayya da zaman lafiya a cikin al’umma.

“Hukumar tana kuma da ƙwararrun jami’ai da su ka ƙware wajen sasanta al’umma a lokacin da su ka samu saɓani.

“Ina son na yi amfani da wannan dama na tunatar da al’umma cewa Musulunci ya yi horo da sasanta tsakanin al’umma.
“Har gwara ma al’umma su sasanta a tsakanin su ba wai sai an je kotu ba,” inji shi.