Mun shirya fito-na-fito da APC — Malami

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami wanda a ranar Laraba ya sanar da ficewa daga jamiyyar APC, ya ce a shirye haɗakar ADC take wajen yaƙi da gwamnatin APC domin kawo “gyara kan yadda ake tafiyar da gwamnati.”

Malami wanda ya kasance minista a zamanin gwamnatin tsohon shugaban Nijeriya, Mumammadu Buhari, ya ce ukuɓar da gwamnati Tinubu ta sanya talakawan Nijerya a ciki ba za ta misaltu ba.

A hirarsa da BBC, Abubakar Malami ya ce sun fito fili ne domin su yaƙi jam’iyyar APC mai mulki, musamman yadda ta bar abubuwa da dama sun tabarbare a ƙasar, ciki har da tsaro da tattalin arziki da kuma sauran dangogin wahalhalu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jefa talakawa.

“A duk lokacin da wata tarayya ta zo da wasu tsare-tsare na ƙuntata wa al’umma, da sanya su cikin halin wahala to wajibi a taru wuri guda su dauki mataki domin kawo sauyi ta hanyar maido da kaykkyawan tsari, da zai ɗaɗa wa mutane,” inji shi.

“Mun yanke hukuncin ɗaukar mataki domin yaƙi da rashin tsaro da ynuwa domin maido da Nijeriya kan turba mai kyau da tsari,” inji Malami.

By ukarofi