Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana mataki da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ke ɗauka na farfaɗo da bunƙasar ilimi da har aka dawo da cigaba da karatu a Kwalejin ilimi ta Ghari da cewa abu ne na mutuƙar jin daɗi da farin ciki ga cigaban al’ummar Jihar Kano.
Dakta Abdullahi Asiru shugaban Kwalejin Ilimi ta Ghari ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce al’ummar ƙaramar hukumar Ghari da na Kano ta Arewa da su da aka ɗorawa nauyi da amana na shugabancin Kwalejin da masu kishin Ilimi a Jihar Kano baki ɗaya na murna da dawo da makarantar duba da yadda a Gwamnatin baya aka yi wa ilimi riƙon sakainar kashi da ta kai ga rufe ta, yanzu zuwan Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ɗauki matakai na farfaɗo da inganta ilimi a Jihar Kano ta dawo da makarantar.
Ya ƙara da cewa Kwalejin Ilimi da share fagen shiga jami’a ta Ghari yanzu ana nan ana ayyuka a cikinta sakamakon alƙawari da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi ana aikin kewaye Kwalejin da katanga da ƙofofi na zamanil.
Ya ce duk wani taimako da Gwamna ya yi alƙawari na inganta Kwalejin an fara ayyuka, kama daga kan samar da kujeru na karatun ɗalibai da ƙoƙarin samar da kayan aiki.Yanzu haka ɗalibai masu karatun NCE na ɗaya da na biyu dana Uku suna nan suna karatu sannan suna shiirin ɗaukar sabbin ɗalibai a Kwalejin Wanda yanzu haka akwai ɗalibai 350 suna karatu.
Ya ce a ƙiyasi nan gaba kaɗan za su ɗebi sabbin ɗalibai sama da 3000 da za suyi kwasa kwasai daban daban da ake gudanarwa a kwalejin ilimi ta Ghari na neman shaidar NCE da na share fagen shiga jami’a.
Dakta Abdullahi Asiru ya ce Gwamnatin Jihar Kano ta yi alƙawarin samar da kayan aiki da malamai ga kuma Kwalejin ta tabbatar da ita ,ba abinda ya rage musu illa su bada gudunmawa wajen bunƙasa ilimi ta tsayawa suyi aiki tuƙuru a matsayinsu na shugabanin kwalejin don cimma manufar Gwamnati na bunƙasa ilimi da yardar Allah.
Ya ce babban fatansu da burinsu Kwalejin Ilimi ta Ghari ta zama zakaran gwajin dafi a Kano ta Arewa, saboda babu wata babbar Kwalejin Ilimi kamar ta ,sannan ƙaramar hukumar Ghari na da kusanci da jihohi biyu ta ɓangaren Kazaure tana da kusanci da jihar Jigawa sannan ta na da kusanci da jihar katsina ta ɓangaren gidan mutum ɗaya wanda zai kasance hatta ɗalibai daga jihohin maƙota za su ci gajiyar samun karatu a kwalejin.
Ya ƙara da cewa Kano ta Arewa tana da aƙalla ƙananan hukumomi 13 don haka nema a Kwalejin suke da shiri na baiwa shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin yankin takardu na ɗaukar ɗalibai kyauta a kwalejin domin su baiwa ɗalibansu da suka cancanta a da za a ɗauka domin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce musu a taimakawa ɗalibai su yi karatu, ba an samar da makarantar ne domin neman riba ba sai don Ilimi .
Shugaban kwalejin Ilimi ta Ghari ya ce makarantar tana da wurin kwanan ɗalibai da filayen wasanni da ɗakunan karatu kuma ɓangaren Mata da na maza daban suna da kuma manyan rijiyoyin burtsatse ba su da matsalar ruwa kuma Gwamnati ta yi musu alƙawarin sanya musu manyan injuna masu zuko hasken rana domin a samarda wuta dan samun cikakken kulawa na koyo da koyarwa.
Sannan a ɓangaren tsaro Kwalejin Ilimi ta Ghari a kusa take da ofishin yansandan yankin har ma shugaban ma’aikata na Gidan Gwamnatin Kano ya haɗa su da shugaban sojoji harma hukumar makarantar ta kai masa ziyara ya yi musu alƙawarin taimaka musu ta sanya sojoji wajen kulada tsaro a kwalejin sannan suna addu’oi na neman kariyar Ubangiji ga makarantar.
Shugaban kwalejin Ilimi na Ghari ya yi nuni da cewa kasancewar Jihar Kano gari ne na musulunci wanda shi ya tsara tarbiyya kyakkyawa, ɗalibansu masu ladabi da biyayya ne, da kuma son karatu.Akwai ma shiri da suke so suyi nan gaba na bada wasu ajujuwa a cikin kwalejin da za a mayar wajen karatun islamiyya, wanda Kwamishinan Ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Kofar Mata ya sahale ayi hakan dan daɗa bunƙasa cigaban Kwalejin.
Dakta Abdullahi Asiru ya ce Allah shine shaida tunda aka basu amanar shugabancin Kwalejin suke ta faɗi tashi da ma’aikatansa, akwai mataimakinsa Hamisu Musa Gambo Ɗanzaki da rijistarar Kwalejin Muktar Shehu Alhayat da mai kulada kuɗaɗenta Mubarak Abba da kuma babbar mai kulada ɗakin karatu Jamila Mansur Chiranci waɗannan mutane biyar dashi kansa kullum tare suke tunda aka buɗe Kwalejin 1/1/2024 basa zama aiki suke kodayaushe.
Ya ce Allah shine masani cikakken burinsu su ga Kwalejin Ilimi ta Ghari ta jera da duk wata Kwalejin Ilimi da ke ƙasar nan, koma ta fita saboda yanzu sun zama cikakkiyar kwalejin Ilimi, kwanan nan dokar su zata fito da aka sahale musu zama cikakkun masu bada shaidar NCE burinsa ya ga ɗalibansu suna gogayya da duk wasu ɗalibai, duk wata shaidar karatu da ake bayarwa a makarantun ilimi a ƙasarnan ya zama daidai da nasu
Ya tuna cewa a lokacinda Kwankwaso yake Gwamnan Jihar Kano ya kafa makarantar Karatun “IJMB, remedial “ake Gwamnatin baya da tazo ta rufe ta, aka daina karatun sai zuwan Gwamna Abba Kabir ya dawo da ita ya buɗe ta aka ƙara mata kima ta zama cikakkiyar kwaleji da suke “NCE,IJMB, Remedial” Nan gaba ma in Allah ya yarda tunda da rarrafe ake tashi har digiri ma sai an yi a kwalejin Ilimi ta Ghari.
Dakta Abdullahi Asiru shugaban kwalejin Ilimi ta Ghari ya ce hatta a ɓangaren bunƙasar tattalin arziƙi makarantar ta Ghari ta bunƙasa Kasuwanci da sufuri da sayar da kayayyakin abinci a garin, hatta gidajen haya zasu bunƙasa ta nan ma an taimaki ƙaramar hukumar wajen ƙarin samun kuɗin shiga da bunƙasar tattalin arziƙi yan garin ma da suke zuwa cirani zasu ragu zasu tsaya suyi sana’oi a garin hatta Mata zasu sami sana’oi ,dama waje ne na noma.A kwasa- kwasai da za suyi akwai na harkar noma da koyon sana’oi da za a riƙa koyawa ɗalibai.
