Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Al’ummar Gaya na alfahari da nuna soyayya da biyayya ga mai martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Abdulƙadir, musamman ganin yadda yake da dattaku da kuma miƙa lamarinsa ga Allah wanda wannan abin koyi ne ga shugabanni da sauran al’umma wanda babu wani abu dake jawo alkairi da zaman lafiya kamar haƙuri da kyakyawan shugabanci a tsakani, don haka al’ummar gaya na farin ciki da alfahari da irin mulkin mai martaba Sarkin Gaya kamar yadda Talban Gaya Alhaji Kamal, ya bayana a wannan lokaci.
Shi ma shugaban ma’aikata na ƙaramar hukumar Gaya ya ce yadda da ƙaddara da abin da Allah ya kawo shi ne abin da ya jawowa Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Aliyu ɗaukaka wanda hakan ce ta sa ya samu dawowa a matsayin Sarkin Gaya bayan da majalisar dokokin Jihar Kano ta rushe sarakuna biyar na Kano a watannin baya da su ka gabata, wannan bayanin ya fito ne daga shugaban ma’aikata na ƙaramar hukumar Haya Abubakar Haruna Bichi, wanda kuma tsohon kantoman Gaya ne a lokutan da ya gabata a wata ganawa da ya yi da manema labarai a ƙarshen makon nan.
Har ila yau ya ce yadda Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da sauran jiga-jigan gwamnatin Kano, da masarautar Kano su ka taka muhimmiyyar rawa ta gudummawa wajen dawo da mai martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir da kuma ba shi sandar kama aiki babu abin da al’ummar Gaya da Kano za su ce sai fatan alkairi na bunƙasar arziƙi da zaman lafiya a masarautar Gaya da Kano da Nijeriya baki ɗaya.
An dai ruwaito masu riƙe da muƙaman gwamnati da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, sarakuna, da sauran al’ummar Gaya na yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan naɗa Sarkin Gaya karo na biyu da kuma alwashin gina kwalejin kimiyya da fasaha a masarautar gaya don bunƙasar ilimi da aikin yi ga matasa, da bunƙasar tattalin arziƙi na wannan yanki na Kano baki ɗaya.
