Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Shugaban rundunar Cibil Difens na Jihar Kano, Muhammad Lawal Falala ya bayyana cewa hukumarsu bisa umarnin Gwamnatin Tarayya na bai wa makarantun ƙasar nan kariya ta fuskar wayar da kai ga shugabanin makarantu, malamai da ɗalibai, wanda ya ce ita ma Kano ba a barta a baya ba wajen bada wannan kariyar tsaro na musamman ga makarantun jihar, inda ya ce wannan na daga cikin aikin rundunar ta NSCDC na ba fararen hula kariya da hana lalata da satar kayayyakin amfanin al’umma na gwamnati da dai sauransu.
SC Lawal Muhammad Falala ya bayyana haka ne wa manema labarai bayan fitowarsa daga ɗakin taro na yini ɗaya da aka shirya ga shugabanin makarantu, malamai da ɗalibai da kuma haɗin gwiwar ma’akatar ilimi ƙarƙashin shugabancin Hon. Umar Haruna Doguwa kwamishinan ilimi na jihar Kano wanda aka gabatar a kwalejin Sa’adatu Rimi a ranar Talata da ta gabata.
Shi ma a jawabinsa kwamishinan ilimi na jihar Kano Hon. Haruna Umar Doguwa ya bada tabbaci cewa ma’aikatar ilimi ƙarƙashin shugabancin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a shirye ta ke wajen bada haɗin kai wajen tabbatar da tsaro a makarantu da ma sauran wurare wanda da ma babbar manufar gwamnatin Kano shi ne samar da tsaro, ilimi, lafiya, noma, bunƙasar tattalin arziki ta hanyar samawa matasa aikin yi wanda ita ma babbar hanya ce ta samar da tsaro a jiha da ƙasa baki ɗaya.
“Don haka wannan aiki na NSCDC abin farin ciki ne da kuma samun goyan baya ɗari bisa ɗari a wannan aiki na bai wa makarantun Kano tsaro.”
A ƙarshe jami’an da suka wakilci hukumomin tsaro da suka haɗa da rundunar ‘yan sanda da DSS da sauransu sun gabatar da jawabi na hikimomi da dabaru da al’umma za ta bada wajen tabbatar da tsaro a makarantu da sauran wurare inda mahalarta wannan taro suka nuna gamsuwarsu na wannan taro tsakanin gwamnatin Kano da hukumar NSCDC Kano.
