Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jakadan Falasɗinu a Nijeriya, Abdul Abu Shawesh ya ce, a rana ta 243 da Isra’ila ta fara wa al’ummar Falasdinu kisan ƙare dangi, ina nuna matuƙar godiya da irin ɗimbin goyon bayan da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ke bai wa Falasɗinawa.
Abu Shawesh ya bayyana hakan ne a ciki wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce; “A yau, zan fara da miƙa godiyata ga Tarayyar Nijeriya bisa tsayuwar daka wajen nuna goyon ƙudurin saka Falasɗinawa a Hukumar Lafiya ta Duniya da aka amince da shi a ranar Juma’ar da ta gabata.”
“Muna sa ran Nijeriya za ta yi amfani da cikakken ƙarfinta na siyasa, wadda ake girmama ta a duniya, don tabbatar da daidaito a fagen siyasar duniya da kuma hana dokar daji.
“A jiya Slovenia ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta bayan da majalisar dokokinta ta kaɗa kuri’ar amincewa da matakin,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Ya zuwa ranar 4 ga watan Yuni, adadin shahidan Falasɗinawan ya kai 36,550, sannan 82,959 sun samu raunuka, inda kusan dubu 10 suka ɓace a ƙarƙashin ɓaraguzan gini da ƙungiyoyin ceto ba su yi nasarar isa wuraren ba. Ya kamata a lura cewa yawancin waɗanda abin ya shafa mata ne da ƙananan yara.”
“A cewar hukumar da ke kula da fursunonin da ake tsare da su tun ranar 7 ga watan Oktoba, fursunonin Falasɗinu 16 ne aka kashe a gidajen yarin Isra’ila saboda tsananin duka, da manufofin rashin kula da lafiya, da kuma azabtarwa.
“Kimanin kashi 55 na dukkan gine-gine a Gaza an lalata su, a cewar wani binciken tauraron ɗan adam na farko da Cibiyar Tauraron ɗan Adam ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNOSAT) ta gudanar.
A kwanakin baya ne Falasɗinawa suka gudanar da bikin cika shekaru 100 da kafa ƙungiyar ‘yan jarida, shekaru 25 gabanin ƙirƙiro da Isra’ila daga yammacin Turai. Falasɗinu ce ƙasarmu ce, aljanarmu.
