Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wata ma’aikaciyar jinya mai suna Lucy Likeh ta ɓace bayan zuwa tashar mota a babban birnin tarayya domin aika wa ƙawarta saƙo.
’Yar shekaru 28 da haihuwa, an ce tana aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta a MKK Plaza da ke Jabi, Abuja, an ce ta je wurin tashar na Zuba don aika wa ƙawarta saƙo zuwa Minna, Jihar Neja, ranar Juma’a.
Bayan ta ziyarci tashar, ba a san inda ma’aikaciyar jinyar take ba, kuma wayarta a kashe.
An ce tana sanye da baƙar wando da baƙar riga da hular feskaf lokacin da aka ganta na ƙarshe.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarau a ranar Laraba, surukin Likeh, Shadrach Obi, ya ce ya kai rahoton faruwar lamarin ga wasu ofisoshin ’yan sanda guda biyu da ke babban birnin tarayya Abuja.
“ƙanwar matata ce, kuma har yanzu ba a san inda take ba. Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ina kan hanyata ta zuwa wurin rundunar ‘yan sanda ta FCT. Ko da yake na kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke kusa da inda take aiki. Na kuma kai rahoto ofishin ’yan sanda na Zuba inda ta je ranar Juma’a.
“Amma wannan ƙoƙarin bai haifar da sakamako ba tukuna, kuma a yau, zan je wurin rundunar don bayar da rahoto,” Obi ya shaida.
A halin da ake ciki, tun da farko Obi ya ba da sanarwar ɓacewarta a shafukan sada zumunta, ya tabbatar da Likeh ta isa tashar ne domin aika wa ƙawarta saƙo zuwa Minna.
Kamar yadda bayanin ya nuna, Likeh siririya ce, matsakaiciya a tsayi, kuma cakulan a launi.
