‘Muna so Nijeriya ta fara amfani da fasaha don kawar da ‘yan bindiga’- Majalisar Dattijai

Spread the love

Daga BUHARI FAGGE

Majalisar Dattijan Nijeriya ta nemi gwamnatin tarayya ta koma amfani da fasahar zamani a yaƙin da take yi da mayaƙan Boko Haram da ƴan bindiga.

Hakan na ƙunshe cikin ƙudurin da Sanata Ali Ndume ya gabatar don ɗaukar matakin gaggawa kan harin da aka kai a yankin Gwoza da yake wakilta.

Bayan doguwar muhawara da aka kwashe sa’o’i ana yi tare da jajentawa kan harin, majalisar ta yarda cewa amfani da fasahar zamani a yaƙin zai kawo ƙarshen masu kai hare-haren ƙunar baƙin wake.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, Majalisar ta amince a ƙara bayar da muhimmanci a yankin tafkin Chadi da dajin Sambisa da Kuma hayin dutsen Mandara.

Da yake bayar da tasa gudunmuwar, Sanata Adam Oshimole, ya ce bai kamata a ƙara wa sojoji kuɗi ba da zimmar samar da makaman zamani da kuma fasaha, yana cewa an ba su kuɗaɗen da suke isassu a wannan lokaci.

Sai dai majalisar ta ƙi amincewa da buƙatar tasa, inda mafi yawan mambobinta suka yi watsi da buƙatar.

“Kazalika, wasu daga cikin sanatocin sun nemi gwamnati ta haɗa hannu da kamfanonin tsaro masu zaman kansu domin cigaba da yaƙi a yankunan Tafkin Chadi da dajin Sambisa da sauran wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro a Nijeriya” inji BBC Hausa.

By Babaji