“Burina littafin da nake son bugawa ya samu karɓuwa”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Asiya Muhammad wata jajirtacciyar marubuciyar onlayin ce daga Jihar Kebbi, tana cikin fitattun marubuta da ƙungiyar Lafazi Writers Association ke ji da su, saboda ƙwazonsu da yadda suke rubutu mai tsari da tsafta. Tun da ta fara rubutun labaran adabi a shekarar 2017, Asiya ta fitar da labarai masu yawan gaske, waɗanda take fitarwa a shafukan sada zumunta, kuma masoya littattafanta ke rige-rigen nema su karanta. A tattaunawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana shirinta na fitar da sabon littafinta da za a buga a takarda nan ba da daɗewa ba, wanda take fatan zai kawo canji a rayuwar mutane da dama.
MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.
ASIYA: Da Sunan Allah mai rahama mai jinƙai.To, da farko dai sunana Asiya Muhammad, amma an fi sanina da Asee Beauty. Ni marubuciya ce, kuma ƴarkasuwa.
Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taƙaice?
Ni dai haifaffiyar garin Birnin Kebbi ce a Jihar Kebbi. Na girma a cikin Kebbi, kuma na yi karatuna na boko tun daga matakin firamare har zuwa diploma. Sannan na yi karatun Alƙur’ani da sauran littattafan addini, har yanzu kuma ana cigaba da neman ilimi. Alhamdulillah.
Wanne abu ne ya faru a rayuwarki lokacin tasowarki wanda ya taimaka wajen inganta tarbiyyarki da tunaninki?
Na samu kulawa sosai da tarbiyya a wajen iyayena. Duk da kasancewar mahaifina ya rasu tun ina ƙarama, misalin shekaru uku ko huɗu, daga bisani sai kuma kulawa da tarbiyyar mu ta koma hannun mahaifiyarmu. Itama kuma ta taka rawar gani sosai wajen inganta rayuwarmu da ganin mun yi karatun boko da na Islamiyya yadda ya kamata. Alhamdulillah, ina alfahari da hakan sosai.
Wanne abu ne ya sa ki ka fara sha’awar rubutun adabi?
Tun ina makarantar sakandire nake sha’awar karanta littattafan Hausa, har ta kai ina zuwa kasuwa in sayo littafi da kuɗina in zo in karanta. Daga nan kuma sai na fahimci ai rubutu wata hanya ce ta isar da saƙo ga al’umma, don haka sai na fara rubutu a littafi. Lokacin ni kai na ban san yadda zan yi rubutun ba, ina dai rubuta abinda ya zo kaina ne da kuma duk wani abu da na ga na yi wanda bashi da amfani ko wanda bashi da kyau, inda wata illa kuma in nuna illar abinda zai iya janyowa. To, da haka na fara.
Ko za ki iya tuna labarin farko da ki ka fara rubutawa?
Kai! Gaskiya yana da wuya in tuna, Amma wanda mutane suka fara lura da shi shi ne ‘Danasani’ wanda na rubuta a shekarar 2017.
Wane ne ya fara koya miki yadda za ki yi rubutu, ko nuna miki ƙa’idojin rubutu?
Wacce ta fara koya min yadda zan yi in yi rubutu ita ce Mss Dazzy, tun a lokacin kuma na samu matsalar waya sai na rasa lambarta, yanzu haka ma nemanta nake yi. Don ba zan iya manta alherinta gare ni ba. Daga ita kuma sai Hafast A. Garkuwa. Bayan ita kuma sai Sadiƙ Abubakar, shugaban ƙungiyar mu ta Lafazi Writers Association. Waɗannan su ne suka buɗe min ido a harkar rubutu.
Wacce shekara ki ka fara fitar da rubutunki kuma kawo yanzu littattafai nawa ki ka rubuta?
Na fara fitar da rubutuna ne a shekara ta 2017, sai dai gaskiya ba zan iya tunawa da yawan adadin labaran da na rubuta ba, amma za su iya kai goma sha wani abu.
Gaya mana sunayen littattafanki, kuma ki yi mana bitar fitattu uku a cikinsu.
Daga cikin littattafan da na rubuta akwai, ‘Danasani’, ‘Wata Rayuwa’, ‘Rayuwar Zamani’, ‘Baƙin Butulci’, ‘Mufeeda’, ‘Laifina Ne’, ‘Ba Zai Aure Ki Ba’, da sauransu.
Daga cikin fitattun littattafaina akwai littafin ‘Laifina Ne’, wanda labari ne da ya shafi wata yarinya da ta kasa gane mai sonta tsakani da Allah, ma’ana wanda zai aureta da zuciya ɗaya, da kuma wanda sha’awarta ce kawai ke kai shi nemanta. Amma sai ta fi sa zuciyarta kan wanda sam babu ƙaunarta a zuciyarsa, don bata ma cikin jerin matan da yake son ya aura.
Yayin da ta shiga wulaƙanta wanda ke son ta da gaske. Tun yana haƙuri yana bibiyar ta har ya haƙura ya je ya auri ƙawarta da ke bata shawarar ta auri mai son ta da gaskiya. A lokacin da hankalinta ya dawo kan mai ƙaunarta tuni ya auri ƙawarta, shi kuma mayaudarin ya yi ɓatan dabo bayan ya gama ɓata mata rayuwa da shaye-shaye da bin maza.
Sai kuma littafin ‘Baƙin Butulci,’ wanda labari ne na wata yarinya da ke ɗauke da wata mummunar cuta wadda ke janyo mata ƙyama a cikin al’umma. Allah cikin ikonsa sai ya haɗa ta da wata baiwar Allah wadda ta yi aure da daɗewa, amma babu haihuwa, kuma mai kuɗi ce sosai, mijinta ma babban mai kuɗi ne. Wannan baiwar Allah ce ta ɗauki nauyin wannan yarinya da mahaifiyarta, har Allah Ya sa ta warke ta zama mutum kamar kowa. Daga ƙarshe kuma sai mahaifiyarta da ita suka nemi su janyo hankalin mijin wadda ta taimake su har suke son su fitar da ita daga rayuwa jindaɗi da take samu a gidan mijinta.
Akwai kuma littafin ‘Wata Rayuwa’, wanda ke ɗauke da labarin wasu ‘yam mata da samari da suka ɗaukar wa kansu wata halayyar bin manyan mutane masu kuɗi, suna amfani da talaucinsu suna saka su safarar miyagun ƙwayoyi. A haka ne ɗaya daga cikin ƴammatan labarin mai suna Tina ta mayar da kanta karuwa, har garin karuwancin Allah Ya haɗa ta da wani Alhaji dake saka yara fitar masa da miyagun kwayoyi har ta kai ga an kama ta shi kuma ya gudu.
Shin kin taɓa buga wani a cikin littattafanki ko duka a onlayin ki ke sakewa?
Duka littattafan da nake rubutawa a onlayin nake fitar da su, amma in sha Allahu akwai wani shiri da nake yi na buga wani daga cikinsu zuwa nan da watan Agusta mai zuwa.
Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne taimako ƙungiyar ke miki a rubuce-rubucenki?
Ina ƙungiyar Lafazi Writers Association ne. Kuma faɗin taimakon ƙungiyar Lafazi a gareni kam ba ƙaramin aiki ba ne, ta kowacce fuska ƙungiyar na taimaka min. Allah Ya ƙara ɗaukaka Lafazi da mambobinta.
Waye a cikin marubuta ya zama miki madubin kwaikwayo a salon rubutunsa ko gogewarsa?
Gaskiya zan iya cewa babu shi. Nafi so duk abinda zan yi in yi shi don karan kaina. Don haka ba na koyi da mutane.
Yaya alaƙarki take da masu bibiyar littattafanki, kuma ta yaya ki ke hulɗa da su?
Akwai fahimta sosai a tsakanin mu. Ina bai wa kowa lokaci da damar faɗin abinda suke so. Misali, idan na yi wani abu cikin littafina suka ga ai abinda zan yi a shafin gaba ya kamata ya zama kaza ko kuma bai kamata in yi kaza ba, duk zan saurare su. Kodayake ba dole ne in yi aiki da ra’ayinsu ko tunaninsu ba, saboda ni tun farko na gama tsara labarina, amma ina saurarensu don in ji shawarwarinsu.
Shin wani makarancin littattafanki ya taɓa baki wata shawara da ta sa har ki ka canza wani tsari da ki ka yi wa labarinki?
A’a, in dai na fara rubutu maganar mutane bata canza ra’ayina, don ni na tsara rubutun tun farko ba tare da na yi shawara da kowa ba.
Yaya ki ke samun jigo ko basirar yin rubutunki?
Ina samun jigo ne daga mu’amalata da mutane. Ina kuma duba yanayin halin da muke ciki da kuma zamani, kafin in fara ɗora ɗan ba a rubutuna.
Wanne littafi ne rubutunsa ya fi baki wahala, kuma wanne ne ya fi miki saukin kammalawa, mene ne dalili?
Littafin da ya fi bani wahala a rubutunsa, wanda har na kai kusan shekara biyu ban kammala shi ba, shi ne littafin ‘A Arewa’. Don har sai da rubutun shi ya fara fita a raina. Dalilin da ya sa na kasa kammala labarin kuwa shi ne, labari ne mai tsayi kuma ya shafi al’ummar Arewacin Nijeriya ne. Kowa ya san yadda kullum abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa a Arewa. Wanda kuma na fi jin sauƙinsa shi ne, ‘Baƙin Butulci’.
Yaya harkar rubutun adabi take a Jihar Kebbi, akwai marubuta sosai ko ƙungiyoyin marubuta?
Harkar rubutu a Jihar Kebbi sai dai mu ce Alhamdulillah! Muna da marubuta sosai, maza da mata. Akwai kuma ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kebbi, inda akasari marubutan mu suke. Sannan muna da wasu ƙungiyoyin marubuta daban-daban. Sannan akwai fitattun marubuta da matasa masu tasowa. Akwai fitattun marubuta irinsu Nabeela Dikko, Leemat Pinky, Billy Galadanci, da irinsu Sadiya Ka’oje.
Su waye aminanki da ku ke zumunci sosai a cikin marubuta?
Suna da yawa sosai har ban san wanda zan kira sunansu ba, domin duk marubuci ko marubuciya ina masu kallon abokaina ne ko ƙawaye. Sai dai akwai wasu daga cikin marubuta da abotarmu take da matuƙar tasiri irin su Sadiƙ Abubakar, Abba Abubakar Yakubu,
Mussadam Idriss Musa, Hafast A. Garkuwa, Hafsat Tukur (RM Hafsat), sai kuma Chamsiya Amadou (Autar Mama).
Shin tun bayan fara rubutunki na kanki, kina samun damar karanta littattafan wasu marubutan?
Sosai ma kuwa, shi ya fi komai sauƙi! Ina ajiye rubutuna in je karatun littafin wani. Ina son karanta littattafan wasu marubutan sosai, kuma ba na jin ƙyashin cire kuɗi in sayi littafi a onlayin, duk da nasan da na gama karantawa shi kenan. Littattafan da nake karantawa yanzu, suna da yawa amma wanda ya fi tafiya da hankalina shi ne ‘Sumayya!’
Wacce rawa manhajojin kasuwancin littattafai irin su Hikaya, Arewabooks da YouTube ke taimaka wa wajen inganta kasuwancin littattafai?
Suna taka rawar gani sosai, don wani marubucin ma ba ka saninsa sai ta hanyar tallar littafinsa da manhajojin ke yi, musanman in ana yaɗa rubutun da ke dauke da hoto da sunan marubucin, inda za ka so ka je don ganin marubucin.
Wanne alheri za ki iya cewa kin samu a dalilin rubutu wanda ba za ki manta ba?
Arziƙin jama’a! Lokacin da na fara rubutu na samu tarin mutane fiye da tunanina, kuma na samu kyauta daga wasunsu. Addu’o’i daga bakin mabiya littattafaina kam ba a magana. Sau da dama ina zaune kawai zan ga saƙo ya shigo wayata ana cewa, don Allah ki ajiye lambata, ina son littafinki. Sannan akwai kyaututtuka da na samu daga ƙungiyoyin marubuta da ma marubutan da dama. Sai godiya ga Allah!
Wanne ƙalubale ne ya fi ci miki tuwo a ƙwarya a harkar rubutu, kuma yaya ki ke tunanin kawo gyara?
Ƙalubalen dai bai wuce na ɓatagarin marubuta ba, waɗanda ke fakewa da rubutu suna ɓatawa masu karatu tunani da tarbiyya. Akwai wani da ya taɓa ce min duk marubuta ‘yan iska ne. Ko da na shiga faɗa don kare martabar marubuta sai ya nuna min wani littafin da wata marubuciya ta rubuta, wanda nasan babu yanda za a yi taso ‘yar cikinta ta karanta wannan labarin.
Hanyar gyara ɗaya ce, su tuba su koma ga Allah, su kuma yi istigifari, don Allah ya tsarkake zuciyarsu su daina yaɗa ɓarna da sunan rubutu. Sai kuma mu bi su da addu’a, Allah Ya shirye su. Don dole sai da addu’a ne za su gyaru. Allah ya shirye mu mu bakiɗaya.
Mene ne babban burinki nan gaba a harkar rubutu?
Babban buri na nan kusa shi ne, littafin da nake son bugawa ya samu shiga da karɓuwa a idon duniya, ba ma ƙasar nan kaɗai ba, ya kuma kawo sauyi ga rayuwar al’umma, musamman wanda aka yi rubutun saboda su.
Ko za ki ɗan gaya mana wani abu game da shi wannan littafi da ki ke shirin fitarwa?
Littafin da nake kan rubutawa yanzu shi ne ‘Babu Maraya!’ Kuma labari ne dake nuni kan illar rashin karatun boko, da kuma fa’idar yin karatun, da ɗaukakar da karatun boko ke kawowa. Akwai kuma illar barace-barace da yawon da yara mata ke yi da sunan talla.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Abinda ruwan zafi bai dafa cikin sauƙi ba, sai ruwan sanyi ya dafa shi!
Na gode.
Masha Allah. Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.