Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya fitar da sanarwar aukuwar lamarin.
Ya bayyana cewa faɗan ya faru ne a ƙauyukan Falale da Kadobe a ƙaramar hukumar jibiya inda yan sai ka sukai taho mu gama da tubabbun ‘yan bindiga a yaƙin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 15.
Dr Ɗanmusa ya ƙara da cewa wannan taho mu gama da yan sa kai su kayi da ‘yan bindigan da yayi sanadiyar mutuwar mutane uku shine yasa ‘yan bindiga suka dawo ɗaukar fansa da aka ƙara samun mutanen da suka mutu.
Amma a cewar sa, jami’an ‘yan sanda,DSS, CWC da masu sarautun gargajiya sun maido da zaman lafiya a yankin.
Kwamishinan sai yayi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankali,a bari jami’an tsaro su kammala bincike.
Ya ce gwamnati ta na sane da halin da mutane suka shiga a yankin musamman iyalan da suka rasa na su, za a tabbatar da adalci da kuma ganin haka bai sake faruwa ba.
Fiye da shekara guda kenan al’ummar ƙaramar hukumar Jibiya ke zaune lafiya sakamakon zaman sasanci tsakanin al’umma da yan bindiga a yankin wannan kuwa ya faru ne irin na mijin ƙoƙarin da gwamna Dikko Raɗɗa ya yi wajan samar da zaman lafiya bana a yankin ba har ma da wasu sassan jihar Katsina.
