Mutane da dama sun mutu, da yawa sun jikkata sakamakon rikicin Fulani da Hausawa a Sakkwato

An shiga halin ɗar-ɗar a yankin Gwadabawa a Jihar Sakkwato sakamakon ɓarkewar rikici tsakanin Fulani da Hausawa mazauna yankin.

Bayanai sun ce rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama haɗi da soja guda.

Wani mazaunin yankin, Aminu Gwadabawa, ya faɗa wa kafar VOA Hausa a hirar da ta yi da shi ranar Asabar cewar, “Mazauna yankin na zaune cikin tsoro sakamakon rikincin ya ci ran wani soja.

“Ɓangarorin da rikicin ya shafa kowannensu na ɗari-ɗarin fuskantar fansa daga ɗaya ɓangaren.”

A cewar wani da ya tsallake rijiya da baya a rikicin, “Fulani sun kai wa ɗan uwana hari da wuƙaƙe, amma yana da siddabarun da kaifi ko tsini ba ya huda shi.

Rahotanni sun ce irin wannan rikicin ba shi ne farau ba a yankin, saboda akan fuskanci makamancin haka a yankin Arewa maso Yamma.