Mahara sun kashe mutum 38, sun jikkata 51 a Binuwai

Aƙalla mutum 38 sun mutu, sannan 51 sun jikkata biyo bayan harin da makiyaya suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Jihar Binuwai.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne ranar Juma’a a wata makarantar firamaren da aka bai wa ‘yan gudun hijirar mafaka a Gundumar Nyiev cikin Ƙaramar Hukumar Guma da misalin ƙarfe 7 na dare.

An ce galibin waɗanda harin ya ritsa da su ƙananan yara ne da muma mata.

A cewar wani ganau, “Sun shiga yankin ne daga ɓangarori daban-daban, sannan suka shiga kashe mutane a sansanin.”

Ihembe Tyubee ya ƙara da cewa, “Hatta waɗanda suka tsere zuwa bakin hanya sai da ‘yan bindigar suka bi su suka kashe.”

Aƙalla mutum 51 aka kwashe su zuwa asibiti a Makurdi, babban birnin jihar don yi musu maganin raunukan da suka ji sakamakon harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *