Tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola ya kwanta dama

Tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Babban Lauyan Nijeriya, Bola Ajibola, ya mutu yana da shekara 89.

Ajibola, wanda shi ne ya kafa Jami’ar Crescent da ke Abeokuta, ya rasu ne a ranar Asabar bayan fama da rashin lafiya na dogon lokaci.

Babban ɗan marigayin, Segun Ajibola, SAN, shi ne ya bayyana rasuwar mahaifin nasa cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Sanarwar ta nuna cewar, “Zuciya cike da alheni da godiya ga Allah Maɗaukaki.

“Mahaifinmu, Prince Bola Ajibola, ya bar duniya da tsakar dare. Muna fata Allah Ya yi masa rahma da Aljanah Firdaus.”

A halin rayuwarsa, marigayin ya yi Ministan Shari’a daga 1985 zuwa 1991 a mulkin soja ƙarƙaƙashin mulkin Ibrahim Babangida.

Ya zama alƙalin Kotun Shari’a ta Ƙasa da Ƙasa daga 1991 zuwa 1994 a Hague, Netherlands.

Haka nan, ya zama Babban Kwamishinan Nijeriya a Birtaniya daga 1999 zuwa 2002.

Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) na shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *