Mutum 15 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Aƙalla ‘yan mata 15 aka rawaito sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya ritsa da su a ƙauyen Dandeji cikin Ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.

Majiyarmu ta ce marigayan, ajali ya cim musu ne a hanyarsu ta zuwa yin itace a wani daji da ke kusa inda jirgin ruwa ya kefe da su da safiyar ranar Talata.

A cewar ganau, sama da ‘yan mata 40 ke cikin jirgin ruwan da hatsarin ya shafa.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce, an gano gwawarwaki 15, yayin da masu aikin ceto na ci gaba da bincike don gano sauran.

Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewar, Shugaban Ƙaramar Hukumar Shagari, Aliyu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar hakan.