Fara fiffiken tururuwa: Game da Sarkin Kano na 14

Daga ALIYU AMMANI
 
Ba yau aka fara tuɓe sarakuna ba a wannan yanki namu na arewacin Nijeriya.

Turawan Mulkin Mallaka sun tumɓuke sarakuna da dama a farkon zuwansu, suka kai su Lokoja ‘exile’.

Bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, gwamnatin Arewa ta warware rawanin Sarkin Kano Sanusi ta tura shi ‘exile’ Azare. Daga baya gwamnatin Kano ta dawo da shi Wudil. 

Da wayonmu, mun ga an sauke Sarkin Muri, Sarkin Musulmi Dasuƙi da Sarkin Gwandu Jokolo.

Duk cikin sarakunan da aka sauke daga gadon sarauta tun farkon zuwan turawa ba mu taɓa gani ko jin abubuwan da muke gani da jin labari a yau ba na tawaye da sunan wayewa wadda samun wuri ya haifar ba kamar na Sarki Sunusi.

Gwamnatin Kano ta tsige Sanusi ta tura shi ‘exile’ wani qauye a Jihar Nasarawa. Abokinsa gwamnan Kaduna ya tashi takanas ta Kano ya je har ƙauyen ya ɗauko shi. Sanusi ya koma Legas da zama. Masoya da masu jaje suna ganin hakan ya yi dai-dai.

Da sannu-sannu tsigaggen sarkin ya mai da Kaduna, inda abokinsa ke gwamna, sabuwar masarautarsa. Yana shigar alfarmar irinta sarakuna masu ci, kuma yana tafiya da fadawa, dogarai da zagagai. 

Waɗannan abubuwan da tsigaggen sarkin ke yi, babu wani sarki da aka tuve a tarihin ƙasar nan tun zamanin turawa zuwa yau da ya taɓa yi. Masoya da masu tausayawa ba su ganin matsala da wannan sabuwar bidi’ar da korarren sarkin ke ƙoƙarin sunnantawa.

Yanzu wannan tuɓaɓɓen sarkin na Kano ya fara zama irin na fada a Kaduna ta ƙasar Zazzau inda abokinsa ke gwamna. 

Ba zaman fadar a Kaduna ta ƙasar Zazzau ba ne abin damuwar Mairubutu, halartar Sarkin Zazzau mai ci da fadawansa fadar ne abun damuwar. 

Da takaici Sarkin Zazzau mai ci, shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna, ya ziyarci fadar korarren sarkin Kano a Kaduna ya zauna bisa kujerar baƙi dogaransa na zube a ƙasa shi kuma korarren sarkin na bisa ƙaragar yana sarautar hotiho a cikin ƙasar Zazzau! 

Ko ba komai wane irin saƙo masarautar Zazzau ke ƙoƙarin aikawa Sarkin Kano mai ci a yau?

Ba laifi ba ne Ambasada Ahmad Bamalli ya ziyarci Sanusi a matsayin abokinsa ko ubangidansa ko abokin ubangidansa gwamna a matsayin sa na Ahmad Bamalli. Amma Sarkin Zazzau mai ci a fadar tsigaggen sarki, bisa kujerar manyan baƙi a ƙasar Zazzau!

Masarautar Zazzau, kamar kowace masaurata a Arewa, da ma duniya, na da shimfiɗaɗdun al’adu da tsare-tsare da tadoji waɗanda ake kiyayewa, kuma duk ɗan Sarkin da ya san sarautar ya san su, kuma yana girmama su ba zai taɓa yi masu karantsaye ba.

Ina ganin ya kamata dattawan masarautar Zazzau su zauna da Sarkin Zazzau su ankarar da shi cewa Sarautar Zazzau tsararriyar aba ce ba jeka-nayi-ka ba, duk da mutane da dama na ganin naɗinsa a hakan. 

Saboda haka, kada neman yardar wani ko neman daɗaɗa wa wani ko burge wani ta sa ya ja girma da daraja da ƙimar masarautar Zazzau cikin juji. 

Allah ke ba da mulki, Ya ba shi, kada ya ɗauka zama ɗan barandar wani ne zai dawwamar da shi a bisa gadon sarautar.

Haka zalika, ya zama wajibi ga dattawan Arewa, musamman masu goyon bayan cigaban tsarin sarautun gargajiya, su cire tsoro ko kwaɗayi ko neman yadda su takawa Sanusi burki.

Su ankarar da shi cewa duk yadda kake maita da ƙulafacin son abu, in ya fita hannunka ya koma ga waninka dole ka ƙauracewa yin duk wani abu da zai zub da ko rage girma da ƙimar wannan abun da ka rasa kuma kake masifar so.

Masoya da masu tausayawa na Sanusi na yi masa fatan ya zama dambu mai hawa biyu. Ya zai ji in ya koma sarautar Kano a gobe, sannan wanda aka cire shi ma ya rinƙa yin irin abubuwan da shi yake yi a yanzu?

Muddin ba a yi wa wannan tufkar hanci ba, to akwai yiwuwar wata rana a tsige wani daga sarauta, in yana da kuɗi da fafa a ji, da abokai gwamnoni ya zo cikin garin da aka cire shi sarautar ya gina ƙasaitacciyar fadar alfarma ya fidda kuɗi shi ma ya yi fauki  dogarai da zagagai da ‘yan barda, ya kuma rinƙa gayyato abokansa sarakuna daga wasu masarautu su rinƙa kawo masa ziyarar girmamawa!

Ammani ya rubuto ne daga Unguwar Shanu a Jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *