‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga uku a Zamfara

’Yan sanda a Jihar Zamfara, sun kashe wasu ’yan bindiga uku a tsakanin ƙananan hukumomin Tsafe da Bakura a jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mohammed Bunu, shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin taron manema labarai da ya shirya a Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin jami’ansu da ’yan bindigar a ƙauyen Gidan Giye cikin Qaramar Hukumar Tsafe, an kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwace bindigogi biyu ciki har da ƙirar AK-49.

“A ranar 3 ga Mayu, 2023 da misalin ƙarfe 2:30 na rana, tawagar ’yan sanda da ke sintiri a hanyar Gusau – Tsafe a ƙauyen Gidan Giye a Ƙaramar Hukumar Tsafe, ta yi kiciɓis da ‘yan fashin daji a kan babura uku kowanne ɗauke da mutum uku.

“Ganin ’yan sanda, sai ’yan bindigar suka buɗe wuta lamarin da ya shafe sa’o’i huɗu ana fafatawa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, daga bisani ’yan sandan sun yi galaba a kan ‘yan bingigar inda suka kashe mutum biyu, sauran kuma suka tsere ɗauke da munanan raunuka.

Kazalika, CP Bunu ya ce, jami’ansu sun kashe wani ɗan ta’adda tare da ƙwace bindigarsa. Lamarin da ya ce ya auku a ranar 4 ga Mayu da misalin ƙarfe 2:10 na rana a ƙauyen Yardadi cikin Ƙaramar Hukumar Bakura, Jihar Zamfara.

Kwamishinan ya bai wa al’ummar jihar tabbacin ‘yan sandan jihar ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu na bai wa rayuka da dukiyar jama’a kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *