Gogewa a aikin jarida shi ne kada mai sauraro ya gane inda aka karkata

Daga TIJJANI MUHAMMAD MUSA

Zan yi ɗan tsokaci a kan wannan maudu’in don na nusar da ma’aikatan jarida na yanzu ko Allah SWT zai sa wasu a cikinsu su ɗauki darasi in sha Allah.

Yan jaridunmu na wannan zamani da yawa sukan kasa bambance tsakanin nuna ra’ayinsu a karan kansu da matsayar gidajen jaridun da suke yi wa aiki sannan kuma su san yadda ya kamace su su gudanar da aiki a matsayinsu na ‘yan jarida. Alhali kuwa kowanne tafiyarsa daban.

Bari in ba da ɗan misali da harkar siyasa tunda yanzu haka a cikin damunarta muke tsamo-tsamo. Za ta yiwu ɗan jarida na da jam’iyar da yake so kuma ya kasance daban da na gidan rediyon da yake yi wa aiki, amma in ya tashi aiki yin aiki sai ya nuna fifikon goyon bayan ra’ayinsa ko na tashar tasu maimakon ya tsayawa a kan ka’idar aikin jarida na kar ya nuna ƙarara ina ya karkata. Wato ya tsaya tsaka-tsaki kenan. 

Da yawa ‘yan jaridunmu na yanzu ba sa iya kame kansu ko bakinsu wajen nuna hamayyarsu ko adawarsu ga wani ɗan siyasa da ya ba su damar su yi hira (interview) da shi ko ya zo ya sayi lokaci a tasharsu don a yi hirar yaɗa manufa ko fashin baƙi da shi. Wanda yin hakan ba daidai ba ne.

Sau da yawa sai ka samu wani ma’aikaci ko ma’aikaciyar gidan radio ko talabijin za su gabatar da wani ɗan takara ko wakilin wata jam’iya maimakon su maida hankalinsu kan tambayoyin da za su haska abubuwan dake akwai sai su ɓuge da neman birge ‘yan jam’iyyar da suke goyon baya su saurari tattaunawar don su ji irin tarawa baƙon nan gajiya da ya yi.

Akwai wata hira da na ta6a ji a wata tasha da ba zan kama suna ba a nan Kano tsakanin wani Mai gabatar musu da shirin siyasa da ya samu wani ɗan siyasa da ya sayi lokacinsa tsawon awa ɗaya don ya gabatar da wani ƙuduri na jam’iyarsa. wAllahi da ɗan jaridan nan ya sa honorabul ɗin nan a gaba sai da na tausaya masa.

Samsam ya hana shi sakat da tambayoyi, ƙalubale, sara sukar ɗan takararsu da jam’iyarsu kai ka ce abokin gabansa ne ba ɗan jarida ba. Har sai da ta kai ta kawo shi baƙon nasu ya koka cewa yaya ya sayi lokaci a tasharsu amma ɗan jaridar nan ya fi shi zaƙewa da surutu ga hamayya da adawa iya tsawon lokacin? Gaskiya ba ai musu adalci ba.

Ɗan jaridan nan ya manta kwatakwata da cewa shi a bakin aiki yake wato ba ruwansa da nuna ɓangaraci ko goyon bayan wata jam’iya ko ɗan takara wato ya yi tambayoyinsa da za su bai wa masu sauraro damar su yanke wa kansu hukuncin ina gaskiyar take dangane da lamarin da aka baza a faifan shirin.

Wallahi da yake ina da yadda zan iya da ɗan jaridar da muka gamu sai da na ja hankalinsa a kan ba haka ake yi ba. Na ja kunnensa na yi masa faɗa cewa musamman da yake yana da digiri a aikin jarida daga jami’a bai dace a ce yana sakin layi haka ba, sai ka ce wani ɗanye shakaf wani sabon yanka rake wanda yake neman makama ko koyon aikin jarida.

Na sha gaya wa ‘yan jarida dake aiki a ƙarƙashina a kamfaninmu sws.comms cewa in suna hira da mutum ko wanene shi, su sani cewa, babban ƙalubalensu a wannan yanayin shi ne ƙwaƙulo bayanai daga bakin baƙon don masu sauraro su jiyewa kunnuwansu wasu bayanan da mutumin nan da so samu ne ba zai bayyana su ba.
Shi xan jarida ya sani, ba shi ake son aji ba, a’a baqon nan da aka gayyato ma fi akasari mutanen gari suke son su ji kuma suka kama tasharsu don su ji mai zai ce ba kai ba. Don haka, tsara tambayoyinka bi-da-bi, daki-daki har ta kai ga duk wata tambaya dake kai-kawo a zukatan masu sauraro ka fiddo ta don samar musu amsarta.

Idan ka iya cimma wannan buri masu sauraro kowa zai shedi cewa ka na da dabarun gudanar da aikinka, ka na da natsuwa ga hankali, basira da hazaƙa kuma ka san me kake yi. Sannan ba tare da ka sani ba, sai ka kama yi shura kowa ya kama zancenka har ta kai wasu da ba su san da kai ba su soma neman su ji wai shin wanene kai, ko wacece wance?

Amma ɗan jarida a ko da yaushe ya dinga hanƙoron dole sai an san shi ko sai ya yi fice har ta kai ya dinga gasa da ‘yan fim ko mawaƙa ko sanannun ‘yan wasa da makamantansu a fagen neman suna ko ya zama seleburiti wanda wannan ba abu ne da ya kamaci ma’aikacin jarida ba. In dai zai ci gaba da yin aikinsa na jarida da inganci da kyautatawa, to ya saurari mutan gari ba da jimawa ba kowa zai kana sunansa

Idan kuma irin waccan shanawar yake so ya yi abu ne mai sauƙi ya ajiye makirafon na aikin jarida ya je ya ɗau makirafon na mawaqa ko na ‘yan gambarar zamani (rappers) da ire-irensu ya hau mumbarin Sharholiya ya kama rera waƙoƙin soyayya, siyasa, ashararanci, zuga, shaye-shaye, luqa ashariya da dai sauransu. 

Nan ba da jimawa ba duk gari za a san shi. Amma aikin jarida ai aiki ne mai matuqar ƙima, muhimmanci, daraja, kwarjini da dai sauransu. 

Bari in ajiye alkalamina a nan. Sai wani jiƙon.

Tijjani M. M. marubuci kuma manazarci ne. Ya rubuto daga Jihar Kano.