Mutumin da ke yi wa ’yan sanda sojan-gona ya shiga hannu a Kano

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wani mutum da ke yin sojan-gona inda yake cutar al’umma.

Mai magana da yawun rundunar a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

SP Abdullahi ya ce an kama mutumin bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga mazauna Fagge da Sabon Gari da Koki da kuma kwaryar birnin Kano, inda suka ce mutumin yana amfani da matsayin jami’in ɗan sanda wajen karɓar kuɗaɗe a hannunsu.

“Mun kama mutumin ne mai suna Salisu Bala mai shekara 31 ranar 14 ga watan Oktoba a Kurna ƙaurters sanye da kakin ’yan sanda inda yake aikata ba daidai ba,” inji Kiyawa.

Ya ce binciken farko da suka fara yi ya nuna cewa mutumin ba shi da alaƙa da ’yan sanda ko kuma wata hukuma ta tsaro, kawai yana sojan-gona wajen karɓar kuɗaɗen mutane.

Kakakin ’yan sanda ya ce sun kuma gano kakin ’yan sanda har kala huɗu a gidan mutumin.

Kwamishinan ’yan sandan jiihar ta Kano, CP Salman Dogo Garba ya ce ba za su lamunci yi musu sojan-gona ba ko kuma wani ya riƙa karɓar kuɗi a hannun mutane tare da sunan jami’in ɗan sanda, inda ya ce za su ci gaba da ɗaukar matakai na kare al’umma daga irin waɗannan mutane.