Nijeriya a hannun ‘yan sari…

Daga UNCLE LARABI

Yanzu Naira 10,000 ba komai ba ce! A ƙaramar bakar leda za a saka maka kayan Naira 10,000. Shekaru biyu baya idan aka ce za a saka kayan Naira 10,000 a bakar leda sai a ƙaryata mutum. Ina ake so talaka ya tsoma ransa ya ji daɗi a ƙasar nan?

Wallahi bala’in ya asa! Birkila ya fita ya yi aikin Naira 5000 a rana. Nawa zai ci a wajen aikin? Sai ya ci abincin Naira 1000 a haka ma ya yi maleji. Nawa zai zo ya ciyar da iyalansa? To, lebura ma Naira 3000 za a ba shi ko Naira 2500. A abinci da kuɗin mota kuɗin za su ƙare fa. 

Ba a maganar masu ƙaramin aiki ko na gwamnati ko na kamfani da albashinsu ba ya wuce Naira 45,000. Akwai kuma mutanen da ba sa aikin ma. Ba sa sana’a ƙwaƙƙwara, buga-buga suke yi, don su ci abinci kowane iri ne su rayu. 

Akwai kuma waɗanda aka kora a aiki na kamfanoni da waɗanda suka cinye jarinsu. Masu ƙaramar sana’a su ma yanzu neman yadda za su ci abinci su rayu suke yi. 

Wace irin ƙasa ce wannan muke rayuwa a cikinta da kullum sai dai a ce gwara baya da gaba. Duk shugaban da ya zo ba ya ƙoƙarin ganin ya gyara ƙasar, sai dai ya gyara aljihunsa. Ba ya tunanin kyautata rayuwar talakawan da yake mulka sai dai kawai ya fantama ya ji daɗi kawai. Shi a tunaninsa shine mulki?

Har lau kuma akwai ’yan kanzaginsu a gefe da ake sam-masu suna lasawa su ne za su fito suna kare su duk irin azabtar da talakawan da za su yi azzaluman shugabannin.

Abdullahi Jibril Dankantoma (UNCLE LARABI), za iya samun a lambar wayarsa; 08065418892, Kano – Nijeriya