Daga AISHA ASAS
Ina mamakin yadda ake mutuwa da yadda mutuwar ke zo wa mutane, amma da yawan mu ba mu rusuna ba.
A cikin kowacce mutuwa akwa faɗakarwar ga waɗanda aka bari, saidai ban san yadda mutane ba sa kallo zuwa ga darussan da ke tattare da ita.
Me ka ke taƙama da shi? Kuɗi ne ko mulki? Kyau ko gata? Dukkansu ba sa iya yi ma shinge da ita yayin da ta zo tafiya da kai.
Riga ce da ke sanye a wuyan kowa, kuma ba wanda ke da ƙarfin iya cire ta, kamar yadda aya a cikin littafi mai tsarki ta faɗa, “Kowacce rai za ta ɗanɗani mutuwa. Kuma Muna jarraba ku da sharri da alheri domin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.”
Idan har mun aminta cewa, wannnan ranar da za mu kwanta, amma mu kasa tashi, ko za mu shiga, mu kasa fitowa, ranar da za a yi mana wanka ba da ra’ayin mu ba, ranar da za a sallace mu maimakon mu sallata, ranar da ɗimbin mutane za su yi bankwana da mu, suna masu gaggawar kai mu nesa da su, don gudun mu kai ga yin wari. Ranar da matanmu masoyanmu za su ƙauracewa shimfiɗar mu, ranar da ‘ya’yanmu za su ji tsoron ganinmu. Ranar da ‘yan uwanmu ke hanzarin kai mu rame su rufe.
Idan har mun amince da akwai irin wannan ranar, me muke jira da ba za mu yi mata shiri ba? Me ya sa ba ma tambayar kanmu me muka tanadarwar wannan rana? Me ya sa muka shagala a kallon hallayar wasu muka manta da namu?
Kaso mafi nauyi na al’umma a yanzu sun fi karkata ga kallon me wasu ke aikatawa tare da yi masu hisabi da bakunsu.
Ya kai bawan Allah, me ka ke da shi da ya ba ka damar yanke wa bawa ɗan’uwanka ƙauna da rahmar mahallicinsa. Idan kaga bawa mai sabo a aljanna me za ka iya yi, kana da damar fitar da shi ne?
Wallahi masu shagala ga kallon aibun wasu na tattare da hasara.
Ya ku bayin Allah, shin ba na ba ku labari ba akan wani bawan Allah makusanci mai aikata saɓo ba. Ya kasance tun a ƙurciya mai yawan faɗa ne, ya kasance mai yawan ɗauko rigima ne, har ya girma ba a huta ba. Babu abinda ya tsira a ɗakin mahaifiyarshi da na sauran mutanen gida. Komai ya gani ya zama nashi. Fitina babu irin wadda ba ya yi, kayan mutane da shaye-shaye. Har ta kai aka yanke masa ƙauna da rahmar Ubangiji saboda yawan shekarunsa a tafarkin.
Saidai kuma, mutum ne ma’abuci sallah, a cikin kowane yanayi zuciyarshi ba ta rinjayar shi wurin barin sallah. Ko a lokacin da yake cikin maye ba ya matanwa da lokacin sallah. Mutum ne ma’abuci kyauta. Ko zai ɗauko kayan mutane ne daga ciki sai ya yi kyauta. Zuciyarshi na yin fari yayin da ya ba wa wani daga cikin abinda ya mallaka.
Mutum ne mai yawan ɓata ran mahaifiyarshi, amma mafi tausaya mata. Sannan ma’abuci tsafta da kusan kullum sai ya yi wanki. Kuma mai yawan azumi. Idan Ramadana ya tsaya kuwa, yana ajiye duk wata shiririta ya fuskanci Ubangijinsa. Amma baya ga waɗannan babu wani abu mai kyau a tare da shi.
Amma abinda zai ba ka mamaki, a daren Juma’a da ta gabata, ya bar gida zuwa nasa gidan don kwantawa, a hanya ya tsaya ya siye maganin gudawa, yana sanar da abokin tafiyar tasa cikinsa ke ciwo. A cikin wannan dare mai albarka gudawa ya ci ƙarfinsa har yana zuba a hanyar zuwansa bayi. A cikin wannan yanayi Allah Ya karɓi bawanSa. Ga shahada ta ciwon ciki, ga daren Juma’a, kuma ya bar uwa a raye da ta yafe masa dukkan ragowar abinda ba ta riga ta yafe masa ba.
To a nan kai me za ka ce? Rahmar Allah mai wanzuwa ce, kuma ta lulluɓe komai da kowa. Idan ya ga dama ya yi maka gafara, idan ya ga dama ya azabtar da kai.
Don haka, ya ku bayin Allah, mu karkata ga yi wa kanmu hisabi tun a lokacin da muke iya gyara wa, kafin mu je inda za a yi mana hisabi tare da sakamako. Mun dai san komawa wurin Ubangiji babu makawa, domin mun san inda mutawa take kai bawa. Kamar yadda Alƙur’ani mai tsarki ya faɗa.
“Ka ce: Mala’ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shi ne ke karɓar rayukanku. Sa’annan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.”
Allah Ya sa mu yi ƙarshe na ƙwarai