Na dawo Musulunci, inji Abdurrasheed JJC Skills

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shahararren mawaƙin nan kuma mai shirya fina-finai, AbdurRasheed Bello, wanda aka fi sani da JJC Skills ya bayyana cewa ya koma Musulunci, addinin da mahaifinsa ke bi.

Tsohon mijin fitacciyar jarumar fina-finai, Funke Akindele, ya bayyana hakan ne ta hanyar wasu rubuce-rubuce da ya wallafa a shafinsa na Instagram da aka tabbatar wanda wata kafar yaɗa labarai ta Musulunci ta yanar gizo mai suna Muslim News ta ruwaito a jiya Alhamis.

JJC Skills ya ce asalinsa haifaffen addinin Musulunci ne, amma bai tava yin hakan ba domin ya zaɓi bin addinin mahaifiyarsa, ya qara da cewa “da ban san inda nake ba, amma yanzu na dawo hayyacina,” inji shi.

‘Ya Allah, Ina roqonka ka gafarta min, ka ƙara mini imani duniya da lahira.

“Ya Allah ka lulluve ni da rahamarka, kuma ka sauƙaƙa mini vacin rai, kuma ka kiyaye ni da komawa abinda na yi a baya, da damana da haguna da sama, kuma Ina neman tsarinka don kada ƙasa ta haɗiye ni.”

Mawaƙin ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Muslim News, inda ya ce Allah ne ya sa zai musulunta daga ƙarshe.

“An haife ni Musulmi, babana Bello Musulmi ne, amma mahaifiyata Kirista ce. A lokacin Ina zuwa Islamiyya amma duk abin da na tuna sai an buge ni. Sun kasance suna tsoratar da mu da wutar jahannama don haka, ban tava yin aiki ba.

“Allah ne ya hukunta zan koma Musulunci. Na gode wa Allah da ya kiyaye rayuwata,” inji JJC.