Nijeriya za ta fara cire tallafin fetur daga watan Afrilu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin shugaba Muhammadu Buhari na iya fara cire tallafin man fetur sannu a hankali daga watan Afrilun 2023, kimanin watanni uku gabanin shirin farko na dakatar da shugaban na kashe kuɗaɗe.

Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na ARISE a gefen taron tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin Davos na ƙasar Switzerland.

Ta bayyana cewa, cire tallafin da alama matsayin duk masu neman shugabancin qasar ne a yaƙin neman zaɓensu na siyasa a babban zaɓe na wata mai zuwa.

Ta ce, “Abin da zai fi zaman lafiya shi ne gwamnati mai ci, wata ƙila a farkon zango na biyu, ta fara cire tallafin man fetur, domin ya fi dacewa idan ka cire shi a hankali fiye da jira a kwashe shi gaba ɗaya.”

Bayan tsawaita wa’adin watanni 18, Gwamnatin Tarayya na shirin kashe Naira Tiriliyan 3.35 wajen biyan tallafin man fetur daga watan Janairu zuwa Yuni 2023.

Sai dai qarin wa’adin ya haifar da cece-kuce a kan amfanin irin wannan kashe-kashe domin zai qara givin kasafin kuɗi na Gwamnatin Tarayya wanda za a samu ta hanyar qarin lamuni da kuma ƙara samun bashin al’ummar ƙasar wanda ya kai Naira tiriliyan 44.06 a ƙarshen Satumban 2022.

A cewar Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya, cire tallafin man fetur na ɗaya daga cikin sauye-sauyen kasafin kuɗi da ake buƙata cikin gaggawa domin ɗaukaka sakamakon ci gaban Nijeriya, wanda ke da matuƙar tauyewa saboda rashin amfani da albarkatun ƙasa.

Ta qara da cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ya son ɗaukar matakan da za su ƙara taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *