Nijeriya ta fi bakiɗayan ƙasashen yammacin Afrika yawan masu zaɓe – Shugaban INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, bayanai da aka samu sun nuna cewa iajeriya na da yawan masu kaɗa ƙuri’a miliyan 16.7 fiye da sauran ƙasashen yammacin Afirka.

Yakubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata da yamma, yayin da yake gabatar da lacca a gidan Chatham da ke Landan, mai taken ‘Zaɓen Nijeriya na 2023: Shirye-shirye da Gudanar da Sahihin Zave da Haɗa Kai’.

“Bisa alƙaluman da aka tattara daga hukumomin zaɓe da ma’aikatun cikin gida a yammacin Afirka, yawan masu kaɗa ƙuri’a a Nijeriya a halin yanzu ya kai miliyan 16.7 fiye da miliyan 76.7 da aka yi wa rajista a duk sauran ƙasashen da aka haɗa, sannan akwai sauran zaɓuka 14 a yankin.

“Wannan yana nufin cewa babban zaɓe a Nijeriya kamar gudanar da zaɓe ne a yammacin Afirka baki ɗaya,” inji shi.

Yakubu ya yi watsi da duk wani hasashe na shirin ɗage zaɓukan da aka shirya gudanarwa a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga Maris, yana mai cewa INEC ba ta tunani ɗage babban zaɓen 2023.

“Za mu ci gaba da gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara,” inji shi. 

Ya ƙara da cewa, duk da cewa akwai gagarumin ƙalubale da kuma tsammanin INEC, hukumar za ta tsaya tsayin daka akan manofofinta.

“Za mu iya shawo kan ƙalubalen kuma mu tabbatar da cewa zaɓen ya ci gaba da inganta,” inji shugaban INEC.

Zavin farko na kayan aikin sarrafa fasahar zaɓe, musamman ma babbar fasahar zaɓe, yana da matuƙar mahimmanci don samun nasara, a cewarsa.

“Mun san cewa ’yan siyasa sukan yi ƙoƙarin lalata tsarin ta hanyar kai hari kan fasahar, da sanya shakku a kan dacewarta, yin watsi da amfani da ita ko kuma neman lalata tsaronta.

“Wannan ya sa aka ƙirƙiri sabuwar fasahar tantance masu jefa ƙuri’a, ta amfani da na’urar lantarki mai suna ‘Bimordal Voter Accreditation System’,” inji shi.