Wa’adin tsofaffin takardun kuɗi: CBN ya ce mutanen karkara kada su damu

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya, CBN a ranar Juma’a a garin Abuja ya bayyana cewa, mutanen karkara su sha kuruminsu game da batun samun sababbin kuɗin kafin nan da 31 ga watan Janairu da tsofaffin za su tashi daga aiki. Domin kuwa an riga an yi musu tanadin da ya kamata.

A cewar Bankin, zai ƙaddamar da shirin canjin kuɗin a ƙauyuka da sauran wuraren da suka kamata a faɗin ƙasar nan daga ranar Litinin don bunƙasa amsar sababbin takardun kuɗin.

Ya ƙara da cewa, za a yi wannan ƙaddamarwar ne don bunƙasa hanyoyin da mutanen karkara za su samu damar yin canjin takardun Nairorinsu.

Babban Banki zai haɗa gwiwa da Bankuna zuba kuɗaɗe (DMB), da kuma wakilai.

A dai cikin wannan jawabi wanda Haruna Mustapha, daraktan CBN na Sashen sanya ido a kan hada-hadar Banki, da kuma Daraktan sashen tsarin biyan kuɗi, Musa Jimoh, suka sanya wa hannu, an bayyana cewa, shirin zai ba wa mutanen karkara damar canza tsofaffin kuɗinsu zuwa sababbin takardu na Naira 1,000, 500 da kuma 200. Haka kuma za su iya canzar kuɗaɗensu i zuwa, takardun Naira 100, Naira 50 da kuma Naira 20 waɗanda har yanzu ingantattun kuɗi ne.

Hakazalika, CBN ɗin ya ba da umarni ga bankuna da lallai kada su sanya kuɗaɗe a injin cirar kuɗin na ATM indai ba sababbin takardun ba.

Kuma bankuna su kula sosai wajen tabbatar da ingancin lambar BVN ko katin zave na masu ajiyar. Kuma a tabbatar da an gudanar da rabon sababbin kuɗin cikin gaskiya da amana.