Yadda Obasanjo ya saɓa alƙawarinsa da IBB na gadon sa a 2003 – Afegbua

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon Kwamishinan Yaxa Labarai na Jihar Edo, Kassim Afegbua, ya bayyana cewa, akwai wani shiri da Janar Ibrahim Badamasi Babangida zai gaji tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a shekarar 2007 amma Obasanjo ya ƙi amincewa da hakan bayan IBB ya hana shirin komawa mulku a wa’adi na uku, shi kuma Obasanjo ya zavi marigayi shugaba Umar Musa Yar’adua, wanda aka shirya zai zama shugaban ƙungiyar yaƙin neman zaven IBB.

Afegbua, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana yadda Obasanjo ya yi wata ganawa da wasu tsoffin shugabannin ƙasa ciki har da Babangida, inda suka yi watsi da buƙatarsa.

Ya ce, gaskiyar tarihi game da takarar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo na masu cikas a ƙoƙarin hawa mulku a karo na uku ya yaɗu sosai.

A kwanakin baya dai Obasanjo ya ce, bai taɓa son wa’adi na uku a kowane lokaci ba, yana mai jaddada cewa da yana son wa’adi na uku, da ya samu, babu mai iya hana shi.

Afegbua ya bayyana cewa, Obasanjo ya nemi wa’adi na uku, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar ya gaza ne saboda rashin samun goyon baya a zavensa a 1999, daga gwamnoni, kafafen yaɗa labarai, da sauran masu ruwa da tsaki.

Sanarwar ta ce, “bayan na tsallake rijiya da baya a wani yunƙurin kashe ni a safiyar ranar 23 ga watan Agustan 2006 da jami’an gwamnati suka yi, sai da na nemi mafaka a wani wuri da ke kusa da babban birnin tarayya Abuja. Kwanaki biyar kafin harin, manyan jami’an gwamnati da kuma tsohon Shugaban ƙasa sun gargaɗe ni da in sa ido sosai, cewa gwamnatin zamanin ba ta da hurumi kan ƙasidu da wallafe-wallafe da dama da na rubuta, suna fallasa ayyukansu na sirri.

Afegbua ya ce, Babangida zai tsaya takara a zaven shugaban ƙasa na 2007, amma Obasanjo ya shiga tashin hankali, kuma bayan wani taron da aka yi, IBB ya sa ya rubuta wa Obasanjo wasiqa ta gaskiya, inda ya qi tsayawa takara.

Ya ce, “lafin gari ya waye Obasanjo ya nemi Umaru Yar’adua ya zama magajinsa. Umaru Yar’adua a matsayin Gwamnan Jihar Katsina, wanda Shugaba Obasanjo bai sani ba, zai zama shugaban yaƙin neman zaven IBB.

Da yake zama kamar zaki mai rauni sakamakon adawar G4, shugaba Obasanjo ya fara aiki kamar sa a wani shagon Chana. Ya tarwatsa aikin Dr. Odili, kuma yana jin cewa Umaru Yar’adua mai fama da rashin lafiya zai dace da shirinsa. Ba sai an ce Umaru Yar’adua ya rayu shekaru uku a matsayin shugaban ƙasa ba, abin da ya ba Cif Obasanjo mamaki kenan.

Afegbua ya ce, “wa’adi na uku makirci ne na Cif Obasanjo amma ya samu cikas. Bayyana cewa ahugaban ƙasa bai taɓa neman wa’adi na uku ba zai zama ƙarya mafi girma a ƙarni. Cif Obasanjo ya kamata ya ba da labarin haƙiƙanin abin da ya faru, kuma ga bayanai, ya ba da hujjar dalilin da ya sa aka yanke wasu shawarwari; maimakon a fake da da ba mu labaran bogi.”