Na gamsu da zaɓin Ogan ɓoye a matsayin ɗan takarar ciyaman na ƙaramar Hukumar Nasarawa – Zannan Kwankwasiyya 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Zannan Kwankwasiyya, jigo a Jam’iyyar NNPP, tsohon babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf akan kasuwanci da cigaban masana’antu, ya bayyana gamsuwa da zaɓin da aka yi wa Hon. Yusuf Imam da aka fi sani da Ogan ɓoye a matsayin ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai inda ya faɗi a matsayinsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi takarar ya ce kamar yadda ya faɗa a baya cewa duk lokacinsa aka yi hukunci za su yi maraba da hukuncin kuma Allah ya yi ba su samu wannan takara ba suna biyayya da jagoransu musamman Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam.

Alhaji Abubakar Yahuza Gama ya jaddada cewa sun gamsu da yadda aka fitar da ɗan takarar sannan ya yi kira ga mutane da suka nuna masa soyayya da goyon baya da ba za su taɓa mantawa da ƙauna da suka gani daga abokan arziƙi ba kuma Allah bai ƙaddara ba akan waɗanda suka ɗan nuna rashin jin daɗinsu su kwantar da hankali su kuma cigaba da baiwa tafiyar su goyon baya musamman yanzu da suka sa jagora Kwankwaso a gaba wajen samun nasararsa ta takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ya ce duk wani kiraye-kiraye da wasu suke na abar tafiyar Kwankwasiyya duk ba shine ba su sunan a cikin biyayya da wannan jagorori sukayi kuma za su yi biyayya da hidima ga wannan tafiya fiye da yanda suka yi a baya musamman don ganin an yi nasara a zaɓuka dake gaba musamman ma na ɗan takarar su da aka tsayar zai yi takara a ƙaramar hukumar Nasarawa Yusuf Imam Ogan ɓoye.

Ambasada Alhaji Abubakar Yahuza Gama Zannan Kwankwasiyya ya ce yana farin ciki da nasara da Ogan ɓoye ya samu kuma zai bada gudunmawa don ganin ya yi nasara da kuma nasarar jam’iyyarsu ta NNPP a zaɓen ƙananan hukumomi da yake zuwa.

By ukarofi