Na janye ƙararrakin ɓatanci da na shigar saboda wa’azin da na ji, inji Akpabio

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayar da umarni ga lauyoyinsa su janye duk ƙararrakin ɓatanci da ya shigar a kotu kan mutane daban-daban, ciki kuwa har da Sanata Natasha Akpoti, yana mai cewa, wa’azin da ya saurara a yayin taron sabuwar shekara ne ya ratsa shi ya ɗauki wannan mataki.

Akpabio ya bayyana hakan ne a cocin Sacred Heart Parish da ke Uyo a ranar Alhamis, inda ya ce a wancan lokaci yana da kusan ƙararraki tara a kotu a kan mutanen da ya zarga da ɓata masa suna.

A cewarsa, ya shigar da ƙararrakin ne kan mutanen da, a ra’ayinsa, suka yi masa ƙazafi tare da zagin sunansa a bainar jama’a.

Sanatan ya ce, yayin da limamin coci ke wa’azi, sai ya ji kamar saƙon ya shafe shi kai tsaye, abin da ya sa ya sake nazari kan matakin da ya cauka. 

Ya ce nan take ya yanke shawarar ba da umarni ga lauyansa da su janye duk ƙararrakin da ke gudana a kansu.

A shekarar 2025, Akpabio, tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, ya shigar da wasu manyan ƙararrakin ɓatanci da suka ja hankalin jama’a, ciki har da wanda ya shafi abokiyar aikinsa a majalisa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. A ƙarshen shekarar, ya kuma shigar da ƙara ta Naira biliyan 200 kan zargin cin zarafin mata da aka yi masa, zargin da ya musanta, yana mai kira ga wadda ta yi zargin da ta gabatar da hujjoji a gaban kotu.

Haka kuma, a farkon shekarar, matar Akpabio ta shigar da ƙararrakin batanci kan Natasha, tana cewa, kalaman da aka yi sun cutar da martabar iyalinsu. Rikicin siyasar tsakanin sanatocin biyu ya tsananta ne bayan Akpoti-Uduaghan ta zargi Akpabio da taka rawa wajen dakatar da ita daga majalisar dattawa a watan Maris na 2025, bayan ta fitar da zarge-zargen rashin ɗa’a a bainar jama’a.

A ɓangarenta, sanatar ta kai ƙarar matakan da aka ɗauka a kanta gaban kotu, ciki har da ƙara ta Naira biliyan 100 kan Akpabio da wasu mutane, bisa kalaman da ta ce sun bata mata suna.

Da wannan sanarwa da Akpabio ya yi a ranar Alhamis, ya janye dukkan ƙararrakin ɓatanci da ke gudana, matakin da ke nuna ƙarshen dogon rikicin shari’a da ya ɗauki hankalin jama’a, tare da fara sabuwar shekara da sabon salo na sulhu da yafiya.

By ukarofi