Naira 100,000 aka biya ni na kai harin bom masallacin Borno, inji wanda ake zargi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani mutum da ake zargin ɗan Boko Haram ne, Ibrahim Mohammed, ya amsa cewa an biya shi kuɗi har naira 100,000 domin kai harin bom a wani masallaci da ke Maiduguri, Jihar Borno, tare da masu ibada a cikinsa.

Maganar ta fito ne a ranar Laraba ta bakin masani kan yaƙin da ake yi da ta’addanci, Zagazola Makama, a shafinsa na ɗ, inda ya ce majiyoyin tsaro sun tabbatar masa da kama Ibrahim ta hannun dakarun Operation Haɗin Kai tare da taimakon mafarauta na gargajiya a Jihar Yobe.

A cewar majiyoyin, Ibrahim ya amsa rawar da ya taka a harin ƙunar baƙin wake da aka kai a Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga Disamba, inda ya ce an tsara harin ne kuma aka aiwatar da shi bisa umarnin shugabannin Boko Haram da ke aiki tsakanin Jihar Adamawa da yankin tsaunukan Mandara.

Da yake magana yayin bincike, Ibrahim ya ce, “Sunana Ibrahim daga Michika a Adamawa. Mun zo Maiduguri ne domin dasa bama-bamai a Masallacin Izala. Shugabanninmu Adamu da Abubakar ne suka turo mu, suka ba mu bama-bamai guda biyu mu dasa a masallacin.”

Harin da aka kai a Masallacin Kasuwar Gamboru ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata masu ibada 325, lamarin da ya jefa birnin Maiduguri cikin firgici.

Ibrahim ya bayyana cewa sun yi anfani da lokacin da masallacin ke rufe domin dasa bama-baman. Ya ce sun shiga bayan sallar Zuhur da La’asar, suna nuna kamar masu ibada ne, inda abokin aikinsa ya fara tono rami a tsakiyar masallacin shi kuma ya tono a gefe.

Ya ƙara da cewa, an ɗaura bama-baman ne tare da saita lokacin tashinsu kafin sallar Magrib. A cewarsa, “Da masu ibada suka taru domin sallar Magrib, bayan raka’a ta farko ne bom ɗin ya tashi. Mun saita shi ya tashi bayan mintuna biyar, nan da nan na gudu zuwa yankin kasuwa.”

A wani abin da ya ƙara tayar da hankali, Ibrahim ya amsa cewa ya dawo wurin bayan tashin bom ɗin, ya yi kaman san gari mai taimako. Ya ce ya taimaka wajen ɗaukar gawawwaki da wadanda suka jikkata zuwa motocin ɗaukar marasa lafiya.

Wanda ake zargin ya ce kai hare-haren ƙunar baƙin wake ya zama aikin da ake biya a cikin ƙungiyar. A cewarsa, ana biyansa kuɗi tsakanin N70,000 zuwa N100,000 a kowane aiki. Duk da haka, ya ce ya yi nadama matuƙa bayan ganin yadda fararen hula marasa laifi suka rasa rayukansu.

Makama ya bayyana cewa Ibrahim na cikin wata babbar tawaga da aka tura domin kai hare-hare daban-daban a Arewa maso Gabas, a wani shiri na haɗin gwiwa tsakanin Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS), Ansaru da Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), domin kai hare-haren ƙunar baƙin wake da na’urorin fashewa.

An kuma ruwaito cewa wata tawagar Boko Haram ƙarƙashin jagorancin wani kwararren mai haza bama-bamai, Munzir Abu Ziyadah, ta shirya harin PBIED guda goma daga yankin sansanin Ali Ngulde kafin aiwatar da harin Gamboru.

Bayan harin, Ibrahim ya ce ya wuce Jihar Yobe domin yin bincike da tantance wuraren sojoji da ƙungiyoyin mafarauta, a shirye-shiryen kai wasu sabbin hare-hare, kafin daga bisani a kama shi.

By ukarofi