Na saci yaro ne saboda gorinta min da ake yi kan haihuwa, inji ɓarauniyat jariri a Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Wata mata da aka yi shelar ta saci jariri, Ibrahim Mohammed mai kwanaki takwas a duniya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) dake Bauchi satin da ya gabata, jami’an tsaro na DSS sun cafke ta.

Wacce ake zargi da satar ta bayyana cewar, ta aikata wannan laifi ne saboda ɓacin rai daga rainin rashin haihuwa da kishiya da ‘yan uwan mijinta suke nuna mata.

Wata mace ce da ta yi burtun shigar jami’ar kiwon lafiya ta sace ɗaya daga cikin tagwayen jariran daga asibiti.

Bayanai da suka gabata sun bayyana cewar, wacce ake zargi da satar, ta ɗauke jaririn zuwa gidan mijinta dake ƙauyen Dull a cikin ƙaramar hukumar Tafawa Balewa, tana mai cewar ta haihu ne, lamarin da mijinta ya yi tur da shi, yana mai umartar ta da ta mayar da jaririn ga duk inda ta ɗauko shi.

An kuma fahimci cewar, da zarar jin wannan labari na vacewar jariri daga asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, kamar yadda kafofin watsa labarai suka yayata, sai kishiyar ɓarauniyar ta yi shela, tare da kai rahoton lamarin wa jami’an tsaro dake ƙauyen na Dull.

Da zarar samun wannan makama, jami’an tsaro ba su yi wata-wata ba, suka garzaya ƙauyen inda suka yi binciken ƙwaƙwab na ɗaiɗaikun gidaje, kuma ba tare da vata lokaci ba suka cafke ɓarauniyar, wacce a yanzu take shan tuhumce-tuhumce a ofishin su.

Wacce ake zargin da wannan ɗan hali, ta bayyana cewar, ba ta taɓa samun haihuwa ba, kuma ta saci jaririn ne saboda wulakaci da kishiyar ta da wasu ‘yan uwan mijin ta suke nuna mata.

Mahaifiyar jariri da aka sace, Bilkisu Alhassan ta bayyana cewar, wacce ake zargin ta bayyana kanta ne a matsayin ma’ikaciyar kiwon lafiya, tare da bayanin ta fahimci jaririn baya samun wadataccen nonon uwa, don haka yana buƙatar madara da wasu ‘yan sinadarai da za su tallafa masa.

Kamar yadda mahaifiyar ‘yan biyun ta ce, matar ta bata tabbacin yin magana da likita dake ɗakin kiwon lafiyar yara na asibitin, wanda ya yi alƙawarin samar wa mahaifiyar jaririn madara da wasu abincin jarirai.

Bilikisu Alhassan ta ce: “Na shaida wa matar cewa mahaifin jariran ya saya masu kayan abinci, amma ta ce ba irin waɗannan ake buƙata ba, suna buƙatar waɗanda suka fi waɗannan inganci.

“Ta tambaye ni wanne ne daga cikin tagwayen babba, sai na yi mata nuni da Ibrahim, sai kawai ta miqa hannayen ta ta ɗauke shi. Ta shaida mun cewar, za ta kai shi ɗakin gwajin yara. Ban fa san ko wace ce ita ba, amma bisa yarda sai nace ta jira surka ta tana zuwa, amma ta yi tafiyar ta da jariri.”

Jaririn dai, an sace shi ne a ranar 21 ga watan Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 4: 30 daga wajen mahaifiyar sa wacce take asibiti wajen kiwon lafiya. Kuma an samu gano jaririn a ranar 27 ga watan na Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 11: 00 na hantsi, kuma an same shi cikin ƙoshin lafiya.

Da yake yin tsokaci akan batun, Hakimin cikin garin Bauchi, Alhaji Nuru Adamu Jumba ya roƙi hukumar gudanar wa na asibitin koyarwar data sake duba tsarin tsaro na asibitin domin kaucewa sake faruwar irin wannan lamari nan gaba.

Hakimi Nuru Adamu Jumba sai ya sha alwashin cewa shugabannin gargajiya a shirye suke kullum suna faɗakar da al’ummai kan lokutan da suka dace da za ake ziyartar majinyata a asibiti.

Malam Shitu Khalid, a madadin iyalan waɗanda aka sacewa jariri, yayi matuƙar yabawa hukumar gudanar wa ta asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na gano gariri da aka yi awon-gaba da shi