Na yi nasarar samar wa mutane aiki albarkacin sana’ata – Munirat Umar

Da sana’a za ki iya share hawayen kanki da kanki”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Munirat Umar da aka fi sani da M-raah’s kitchen, yar kasuwa ce da ta shafe shekara 7 tana sana’ar hannu kala daban-dadan, munirat Umar ‘yar boko ce da ta karanci Tsumi da Tanadi, wato Accounting. Sai dai bata bari kwalin digirinta ya hanata yin sana’a ba, don dogaro da kai. Jajirtacciyar mace da ta yarda sana’a mafita ce ga matsalolin rayuwa musamman ma ga ‘ya’ya mata. A hirarta da wakilin Blueprint Manhaja a Kano Ibrahim Hamisu, ta bayyana masa yadda ta fara sana’a da kuma irin yadda ta samarwa da ma’aikata guda 5 aiki a wannan masana’ata ta ta. Ku biyo mu don karanta cikakkiyar hirar:

BLUEPRINT MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki.

MUNIRA: Sunana Munira Umar, wacce aka fi sani da M-raah’s kitchen da bedding decorations. Ina da aure da kuma yara.

Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?

To, alhamdu lillah. Na yi primary a Tekond international school zariya, Sannan na yi ‘Secondary school’ a makarantu guda uku, na yi JS1 a Royal college zariya, na yi JS2 da 3 a FGGC Bakori, sannan na ƙarasa SS1 zuwa SS3 a Demonstration. Ban tsaya iya nan ba, domin na samu damar zuwa jami’a, kuma na karanci accounting, wato Tsumi da Tanadi a Jami’ar ABU zariya.

Wacce sana’a kike yi?

Ina sana’a kala biyu zuwa uku. Ina harkar girke-girke wato ‘catering services’, sannan ina harkar kayan fulawa, wato ‘baking’, baya ga haka, ina sana’ar yin yagot, ingantaccen Yoghurt wanda ba a sa masa ‘preservatives’, ɗari bisa ɗari na madara. Kuma Ina yinsa a nau’oi da dama, ina yin ‘plain’, wato fari wanda ba shi da kala, sai kuma ina yin mai kala, ma’ana mai filebo, (flavored) kamar na ‘ya’yan itacen strawberry da Vanilla, sannan Ina yin me sugar da mara sugar. Sana’o’in na wa ba su tsaya iya nan ba, domin ina harkar ‘interior’, watau Ina saida zannuwan gado, filon ƙawar kafet da kujeru, wato ‘throw pillows’, kayan kicin, kayan ƙawata ban-ɗaki da na amfani a cikin sa, kayan jarirai da timtim da kuma labule.

Me ya ja ra’ayinki kika fara waɗannan sana’o’in?

Abinda ya fara bani sha’awa na fara sana’a shi ne, da farko dai sana’a na matuqar birge ni, duba da ɗinbin alfanun da ke tattare da ita, ga kuma uwa uba, bana son inga Ina zaune haka kawai bana komai, domin zaman shiru bai da amfani. Baya ga haka, ta hanyar sana’a ce za ki iya share hawayen kanki da kanki, domin mutum zai iya ɗauke wa kansa wasu qananan buƙatun rayuwa na yau da gobe.

Masara

Yaushe kika fara sana’a?

Na fara sana’a tun a shekarar 2015.

Da kuɗi kamar nawa kika fara wannan sana’a?

To, a lokacin da na fara sana’a na fara ta da kuɗi kimanin Naira dubu ɗari biyu da Hamsin (250,000).

Daga lokacin da kika fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori kika samu?

Alhamdu lillah. Gaskiya nasarori an same su da yawa, domin na yi tattalin jari daga ƙarami zuwa madaidaici. Baya ga haka, sana’a ta ta zama silar samun aiki ga mutane da dama, wato na yi nasarar samar wa mutane abin dogaro da kai ta hanyar tayani aiki na biya su.

Ƙalubale fa akwai ko babu?

To, babban ƙalubale da na fi fuskata ta ɓangaren ‘yan bashi ne. Masu ɗaukar sana’arka cikin yarda da farin ciki a tsakanin ki, amma wurin biya labarin sai ya canza.

Ta yaya kike haɗa kula da yara da maigida da kuma kasuwanci?

Da farko ba abinda zan ce sai alhamdu lillah. Baya ga haka, ka san shi komai tsari yake so, idan ka tsara abu da kyau zai tafi daidai da izinin Allah. Sannan kuma maigidana yana bani haɗin kai kuma yana tayani tsara harkokina.

Ta wacce hanya kike sayar da kayanki?

Ina saida kayana ta hanyar ‘online’, wato shafin whatsapp da instagram .

Abinci

Kina da ma’aikata kamar nawa?

Ina da ma’aikata a ƙalla guda biyar.

Mene ne kiranki ga al’umma musamman mata akan muhimmancin yin sana’a ko yaya ta ke?

Kirana ga mata ‘yan’uwana shi ne, mu dage mu koyi sana’a, saboda tana da daɗi, tana da rufin asiri, tana hana zaman banza.

Na gode.

Ni ma na gode ƙwarai.