NAHCON ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 – Arabi 

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Malam Jalal Arabi, Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ya bayyana cewa hukumar ta fara shirye-shiryen aikin hajjin 2025. Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda-Usara, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, ta ce Arabi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bankwana da rukunin ƙarshe na maniyyatan Nijeriya a ƙasar Saudiyya.

Shugaban NAHCON ya bayyana fatan hukumar za ta samu gagarumar nasara wajen gudanar da aikin hajjin 2025 bisa ga darasin da aka koya a bana. Arabi ya kuma miƙa godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa nasarar kammala aikin dawowar Hajjin 2024.

Ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki bisa haɗin kan da suke bayarwa da kuma alhazan da suke yi wa shugabanninsu addu’a a matakin tarayya da jiha. Shugaban hukumar ya buƙace su da su cigaba da yi wa shugabanninsu addu’o’in samun nasara da kuma ci gaba da ɗa’a.

Arabi ya bayyana nasarorin aikin Hajji na 2024 a matsayin wani alƙawari da ya cika. A cewarsa, a zangon farko na aikin Hajjin 2024, NAHCON ta yi jigilar jimillar jirage 121, wanda a yanzu an rage zuwa jirage 119 na dawowar jirgi.

Ya bayyana cewa an danganta raguwar tashin jirage ne saboda yadda ake amfani da kujeru a lokacin tafiye-tafiyen na dawowa. Arabi ya ce, tafiya ta dawo ta ƙare ne kwanaki uku gabanin lokacin da aka tsara, wanda tunda farko aka shirya kammalawa a ranar 19 ga Yuli.

“Kamfanonin Jiragen Sama na Hukumar sun ɗauki kwanaki 27 don jigilar dukkan alhazai zuwa cikin Masarautar a zangon farko na aikin Hajji, inda a yanzu an kwashe kwanaki 25 ana dawowa.

By ukarofi