NANS ta rushe shugabancin ɗalibai a Ogun

Spread the love

Daga WAKILINMU

Kungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) ta rusa shugabancin ƙungiyar ɗalibai mazauna makarantu ta jihar Ogun sakamakon rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa.

NANS ta kuma kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin gudanar da sabon zaɓe cikin kwanaki 30 masu zuwa

Matakin ya biyo bayan abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin “bincike mai zurfi, adalci da kuma bin tsarin doka” kan jerin ƙorafe-ƙorafe da suka biyo bayan shugabancin ƙungiyar na tsawon watanni.

A cikin wata sanarwa da Shugaban NANS, Olushola Oladoja, ya sanya hannu a ranar Talata ƙungiyar ta ce rikicin ya samo asali ne daga “kuskuren fahimta na kundin tsarin mulki, rashin daidaito a gudanarwa da kuma ƙaruwar rarrabuwar kai.”

NANS ta ta kuma bayyana cewa shugaba mai barin kujerar an zaɓe shi bisa ƙa’ida a watan Fabrairu na shekarar 2025 kuma ya cika dukkan sharuɗɗan doka a lokacin zaɓen ba tare da wani ƙorafi ko ƙalubalantar nasararsa ba, wanda hakan ke tabbatar da ingancin wa’adinsa na farko.

Sai dai, NANS ta yi tir da shugabancin saboda ya tsawaita wa’adinsa fiye da watanni 12 da kundin tsarin mulki ya ƙayyade, har ya shiga wani yanayin sauyi na watanni uku da ya kusa ƙarewa ba tare da bin ka’ida ba.

Sanarwar ta ce kwamitin bai gudanar da taron majalisar ɗalibai kafin babban taro ba a cikin lokacin da ake buƙata, kuma bai kafa kwamitin shirya babban taro na wanda a shi ne za a zaɓi sabbin shugabanni.

Wannan lamari ya nuna yadda ake yawan samun ƙalubale a tsarin shugabancin ƙungiyoyin ɗalibai a Nijeriya, inda sabani kan wa’adin shugabanci, tsarin zaɓe da fassarar kundin tsarin mulki ke haifar da rarrabuwar kai, wanda ke sa hukumomin ƙasa kamar NANS shiga tsakani.

By ukarofi