Kungiyoyi sun gargaɗi gwamnati kan barazanar matsalar tsaro da talauci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyoyin farar hula (CSO) da dama sun bayyana cewa Nijeriya na daf da faɗawa cikin matsananciyar matsala, inda suka yi kira ga shugabanni da al’umma gaba ɗaya da su tashi tsaye domin ceto ƙasar daga halin da take ciki. 

Wannan kira na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka bayyana damuwa kan yadda matsalolin tsaro, talauci da taɓarɓarewar ɗabi’a ke ƙara tsananta a ƙasar.

ƙungiyoyin sun ce suna magana ne a matsayin masu kare dimokiraɗiyya, haƙƙin ɗan Adam da kuma kyakkyawan shugabanci, ba tare da nuna son kai ga wata jam’iyya ba. Sun bayyana cewa a halin yanzu al’umma na fama da asara iri-iri, yayin da ‘yan siyasa ke ci gaba da fafatawa da kalamai ba tare da kawo mafita ba.

A cewarsu, a jihohi kamar Zamfara, manoma da rikice-rikice suka raba da gonakinsu na rayuwa cikin talauci a sansanonin ‘yan gudun hijira. A birnin Abuja kuwa, akwai malamai da ke kashe rabin albashinsu wajen sufuri, yayin da a Legas wasu iyalai ke rage cin abinci domin biyan haya. Duk da haka, gwamnatoci na ci gaba da samun kuɗaɗe masu yawa daga kasafin kuɗi da rabon arzikin ƙasa.

ƙungiyoyin sun nuna cewa siyasa ta zama babbar sana’a a Nijeriya, duk da cewa talakawa na kara talaucewa. Sun ce cire tallafin mai, sassauta darajar Naira da kuma ƙara bashin gwamnati sun ƙara yawan kuɗin shiga, amma ba a ga sauyi mai ma’ana a rayuwar al’umma ba. Sabis na gwamnati na tabarbarewa, banbanci tsakanin masu arziki da talakawa na ƙaruwa, yayin da ‘yan siyasa ke cin gajiyar tsarin.

Sun kuma lissafo manyan matsalolin da ke addabar ƙasar, ciki har da rashin tsaro da kashe-kashe, yawaitar garkuwa da mutane, lalacewar harkar noma da yunwa, takaita ‘yancin faɗin albarkacin baki, cin hanci da rashawa, da kuma taɓarɓarewar tsarin shari’a. Haka kuma sun nuna damuwa kan barazanar da ke fuskantar dimokiraɗiyya, musamman dangane da zaɓen 2027.

ƙungiyoyin sun ce dole ne gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance waɗannan matsaloli. Sun buƙaci a tabbatar da adalci a tattalin arziki, a inganta tsaro, a yaƙi cin hanci da rashawa ba tare da nuna son kai ba, a kare dimokiraɗiyya daga lalacewa, a mutunta haƙƙin jama’a, da kuma sake gina amincewa da tsarin shari’a.

A ƙarshe, sun jaddada cewa al’ummar Nijeriya na ci gaba da biyan kuɗin kura-kuran siyasa, kuma lokaci ya yi da shugabanni za su daina siyasa a kan rayuwar jama’a. Sun ce duk wani kuɗin gwamnati dole ne ya bayyana a rayuwar talakawa, in ba haka ba cin amana ne.

Kungiyoyin sun nuna cewa suna tare da duk wani ɗan Nijeriya da ke fama da yunwa, rashin tsaro da rashin fata, tare da jaddada cewa lokaci ya yi da za a fifita jinƙai da adalci a kan siyasa.

By ukarofi