Bayan wata biyar, ɓangaren Wike na PDP ya karɓe iko da sakatariyar jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bayan watanni biyar da rufe sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Wuse Zone 5 a Abuja akan rikicin jagoranci, hukumar ‘yan sandan Nijeriya ta buɗe shi.

An damƙa sakatariyar da ke Wadata Plaza ga tsagin Ministan Abuja Nyesom Wike, ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, wanda shi ne sabon zaɓaɓɓen shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Tun a watan Nuwamba ne aka garƙame ofishin akan rikicin shugabanci tsakanin tsagin su Tanimu Turaki (SAN) da kuma kwamitin kula da jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed.

A yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta bayar da damar cigaba da amfani da ofishin, wanda a baya ta hana ‘yan jarida, mambobin jam’iyya da jagorancinta shiga na tsawon watanni.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Hon. Jungudo Haruna Mohammed a wata sanarwa ya tabbatar da cewa an sake buɗe ofishin kuma an mayar wa jami’an jam’iyyar ikon kula da shi.

Ana sa ran wannan mataki ya yi sanadiyyar dawowar cigaba da gudanar da harkokin jam’iyyar yadda aka saba a baya a hedikwatar.

By Babaji